
Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite, ta zayyana muhimman shirye-shirye da nufin bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi a gwamnatin Tinubu.
Ta ce ma’aikatar ta taka rawar gani wajen tattaunawa kan yadda Najeriya za ta shiga Yankin Kasuwanci cikin ‘Yanci na Nahiyar Afirka, AFCFTA, sanin yiwuwar ta na fitar da kaya iri-iri zuwa ƙasashen waje, da faɗaɗa hanyoyin shiga kasuwanni, da kuma ƙarin zuba jari kai tsaye a ƙasashen waje.
“Shirye-shirye da yawa na harin sauye-sauye a fagen kasuwancin kayayyaki, da samar da kyakkyawan sakamako ga manoma da masu haƙar ma’adinai.
“Haɓaka ayyukan Kasuwancin Kayayyakin Najeriya, NCX, ƙwararrun shirye-shiryen ta na wayar da kan jama’a, da kafa Cibiyar Ayyuka ta Ƙasa na daga cikin ƙoƙarin da ake yi.
“Musamman, shirin Skill-UP Artisans, SUPA, yana da nufin ƙarfafa masu sana’a miliyan goma da ƙwarewa ta fasaha da takaddun shaida na masana’antu, magance giɓin fasaha da kuma rage dogaro ga shigo da aiki daga waje”, in ji ta.
Anite ta jaddada ƙudurin ma’aikatar don samar da sabbin hanyoyin warware matsaloli da haɗin gwiwar ɓangarori daban-daban.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, wanda ya jagoranci taron manema labarai karo na biyu (MPBS) wanda ya ƙunshi Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, ya ce, “Mun taru a nan don karafa aminta da tabbatar da an sanar da Jama’a r Najeriya.
“Wannan kafa yana ba ku, kafofin yaɗa labarai, damar yin magana kai tsaye da manyan jami’ai kuma ku yi musu tambayoyi game da alhakin su.”
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Mista Bayo Onanuga, da Sakatariyar Dindindin na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dr Ngozi Onwudiwe, da kuma Shuwagabannin hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatun biyu.