Back

Gwamnatin Tarayya za ta buɗe gidan yana na neman lamunin ɗalibai

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za a buɗe gidan yana na neman lamunin ɗalibai a ranar Juma’a 24 ga Mayu, 2024.

Kakakin Hukumar Ba Da Lamuni na Ilimi ta Nijeriya, (NELFUND), Nasir Ayitogo, ne bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Shirin lamunin ya bawa ɗalibai damar samun lamuni don cimma burinsu na ilimi ba tare da matsalolin kuɗi ba.

Sanarwar ta ce: “Hukumar Ba Da Lamuni na Ilimi ta Nijeriya,, (NELFUND), ƙarƙashin jagorancin Manajan Darakta, Mista Akintunde Sawyerr, ta yi farin cikin sanar da ranar 24 ga Mayu, 2024, a matsayin ranar da za a buɗe gidan yana na neman lamunin ɗalibai.

“Wannan ya nuna wani gagarumin ci gaba a yunƙurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR) na samar da ilimi ga duk ɗaliban Nijeriya. Ta hanyar gidan yanar, ɗalibai yanzu za su iya samun rance don cimma burinsu na ilimi ba tare da matsalolin kuɗi ba.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?