Back

Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfado Da Ayyukan Gidaje 46 Da Aka Yi Watsi Da Su A Fadin Kasar Nan

Bankin jinginar gidaje na Najeriya FMBN ya kaddamar da wani shirin gyaran fuska domin farfado da ayyukan gidaje kusan ar’ba’in da shida da aka yi watsi da su a fadin kasar.

Bankin ya ce, za a cimma hakan ne ta hanyar hadin gwiwa da bankin Shelter Afrique, wanda wata cibiyar hada-hadar kudi ce ta nahiyar Afirka da ke ba da goyon baya na musamman kan gina gidaje da gidaje a Afirka.

Babban Manajan Darakta na FMBN, Shehu Usman Osidi ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin gudanarwar bankin Shelter Afrique a kwanan baya a Abuja, inda ya ce bankin ya ba da fifiko wajen farfado da gine-ginen gidaje.

A cewar shi, karfafa hadin gwiwar zai taimaka wajen samar da kudade na gine-gine da jinginar gidaje ga masu zuba jari kan gina gidaje a Najeriya.

Ya ce, “Najeriya na da ayyuka sama da ar’ba’in shida da aka yi watsi da su a jihohi talatin da shida na ƙasar nan kuma FMBN ta kuduri aniyar farfado da su.

“Binciken da muka samu ya nuna cewa bankunan sun kulla yarjejeniyar bayar da kudadden gidaje da jihohin da ake sa ran gwamnatocin jihohi za su samar da ababen more rayuwa, amma abin takaicin shi ne jihohi da dama sun sauya lamarin sun yi watsi da ayyukan.”

“Mun binciki kayayyakin da bankin Shelter Afrique ya bayar kuma mun gano cewa suna bayar da tallafin kayayyakin more rayuwa, don haka muna so mu Yi tafiya da su domin bayar da wannan kudade don mu kammala ayyukan wadannan gidajen mu kuma mika su ga ‘yan Najeriya da dama da ke bukatar matsuguni.”

Osidi ya kuma kara da cewa, Najeriya, kasa ce ta biyu mafi karfin hannun jari a bankin da ke rike da kusan kashi goma sha biyar cikin dari, za ta binciki wuraren da za ta samar da kudade domin cimma burinta na samar da gidaje dubu dari ga ‘yan Najeriya a bana.

Ya kara da cewa, a halin yanzu FMBN na nazarin takardun fahimtar juna da aka yi watsi da su a baya da suka rattaba hannu da kungiyar. Wannan bita na da nufin gano fa’idar da ‘yan Najeriya za su iya samu daga wannan sabon kawancen.

Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Kamfanin Shelter Afrique, Thierno-Habib Hann, ya ce kungiyar ta zo Najeriya ne domin inganta manufofin ta na samar da kudaden raya kasa ta kuma bayyana Najeriya a matsayin inda za a zuba jari da sama da dala biliyan ashirin da biyar a duk shekara.

Ya ce, “A shirye muke mu hada kai da FMBN da sauran cibiyoyi a fadin Najeriya domin magance gibin gidaje. Akwai Kalubale suna nan, kuma dama can ma suna nan.”

 A matsayin mu na cibiyar hada-hadar kudi don ci gaba, muna da kyakkyawar damar hada kai da gwamnatin Najeriya, kuma a wannan tafiya mun gana da dukkan shugabanni ciki har da mataimakin shugaban kasar tarayyar Najeriya mai cikakken himma wajen ciyar da wannan fanni gaba.”

A halin da ake ciki, bankin ya ce ya tara kusan Naira biliyan dari a cikin kudaden da aka tura ta asusun ajiyar gidaje na kasa a shekarar bara.

Bankin jinginar gidaje na Najeriya ne ya kafa shirin NHF domin saukaka ci gaba da tafiyar da kudade masu rahusa domin zuba jari a cikin gidaje na dogon lokaci, ta hanyar cire kashi biyu da digo biyar cikin dari a duk wata daga ma’aikatan da ke samun cikakken albashi.

Tsohon Manajin Darakta na FMBN, Madu Hamman, ya bayyana haka a cikin takardar mika mulki da wakilin mu ya samu.

Ya ce, “Babban nasarorin da muka samu a cikin watanni ashirin da biyu da suka gabata sun hada da cewa a karon farko, a shekarar bara asusun kula da gidaje na kasa da aka tara wa bankin ya zarce Naira biliyan dari. Wannan shi ne karo na farko a tarihin bankin da ake tarawa shekara.”

“Dole ku yi tunani sosai kan yadda za ku iya biyan bukatun masu bayar da gudummawar da yawa a cikin shirin, ta hanyoyi dabam-dabam na bunkasa kudi, wanda ya kamata ya hada da fita waje da NHF saboda idan muka ci gaba da dogara ga NHF. hakan ba zai yiwu ba.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?