Cibiyar Bincike da Maganin Ciwon Daji ta Ƙasa (NICRAT) tana aiki don kafa asibitin rigakafin cutar kansa a kowane yanki na yanki shida na ƙasar.
Babban Daraktan Cibiyar, Farfesa Usman Malami Aliyu, ne ya bayyana hakan a ƙarshen mako a Abuja yayin wani taron kwana ɗaya da cibiyar ta shirya wa ‘yan jaridun lafiya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ‘Yan Jarida Kiwon Lafiyar Jama’a ta Ƙasa da Ƙasa (ISMPH).
Ya koka da ƙarancin asibitocin da ‘yan Nijeriya za su iya zuwa musamman domin auna cutar daji, inda ya ƙara da cewa za a horar da ma’aikatan kiwon lafiya a zaɓaɓɓun manyan asibitocin da za a gudanar da rigakafin kuma za a samar da na’urorin tantance mama, na’urorin hoto da dai sauransu.
Ya ce, “Tare da kafa waɗannan asibitocin tantancewa, muna da niyyar samar da wuraren da mutane za su iya shiga domin likitoci su duba su don gwaji da rigakafi kawai.”
Ya ce hukumar ta ba da fifiko wajen kafa sabbin asibitocin rigakafin cutar daji guda shida domin rigakafin na da matuƙar muhimmanci a al’amuran cutar daji.
Ya ce hukumar ta kuma haɗa hannu da Hukumar Kula da Lafiya na Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA) domin horar da ma’aikatan kiwon lafiya don samar da wasu matakan da suka shafi cutar daji a matakin kiwon lafiya na matakin farko.