Back

Gwamnatin Tarayya za ta kama masu zagon ƙasa ga tattalin arziƙin ƙasa – inji Ministan yada labarai 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce gwamnati za ta kama masu zagon ƙasa ga tattalin arziƙin ƙasar.

Wannan dai na zuwa ne yayin da Idris ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa sauye-sauyen da gwamnatin ke yi na samun nasarori.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu.

Ya ce, “Tun bayan cire tallafin man fetur, shigo da man fetur ya ragu da kashi hamsin cikin ɗari, wanda ya kai lita biliyan ɗaya a kowane wata, kamar yadda Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar. Hakazalika, samar da ɗanyen mai yana ƙaruwa akai-akai, inda ya ƙaru zuwa matsakaicin ganga miliyan ɗaya da hamsin da biyar a kowace rana a cikin rubu’i na huɗu na shekarar da ta gabata, daga ganga miliyan ɗaya da ashirin da biyu a kowace rana a rubu’in da ya gabata.

“Haka zalika, kuɗaɗen wata-wata da Jihohi ke samu daga Kwamitin Raba Kuɗaɗe na Asusun Gwamnatin Tarayya (FAAC) ya ƙaru tun bayan cire tallafin, inda ya baiwa gwamnatoci a dukkan matakai biliyoyin Nairori domin isar da ribar dimokuradiyya ga ‘yan Najeriya.

“Yana da kyau a ce cire tallafin man fetur wani ƙuduri ne na siyasa da dukkan manyan ‘yan takara uku suka yi ittifaki a kai, a cikin saƙon yaƙin neman zaɓen su. Don haka abin ban mamaki ne a ga mutanen da suka yi ta jayayya a cire tallafin, a yanzu suna nuna adawarsu akan sa a yau. Wannan rashin gaskiya ba alheri bane ga ƙasarmu da dimokuradiyya.

“Bayanin da shugaba Tinubu ya yi na biyu shi ne alƙawarin da ya yi na cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) zai yi ƙoƙarin samar da kuɗin musaya ɗaya. Dangane da hangen nesansa na tabbatar da tsarin kuɗi na gaskiya da adalci, amma ba tare da yin watsi da ‘yancin kai na aiki ba, CBN ya ɗauki matakin da ya dace na sassauta iko da canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, da ba da damar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje a farashin kasuwa bisa ƙa’idar ‘mai son sayarwa mai son siye.’

“A matsayinmu na gwamnati, ba mu yi tunanin cewa waɗannan manufofin masu sauƙi bane, ko kuma cewa babu wani abu da ake buƙata. Mun fahimci cewa waɗannan su ne ginshiƙan manufofin kasafin kuɗi da na kuɗi, waɗanda a yanzu dole ne mu gina babban tsarin ci gaban tattalin arziƙi da wadata na gaske akan su.

“Kamar yadda masana tattalin arziƙi suka yarda, waɗannan sauye-sauyen tushen za su kasance masu wahala da zafi ga ’yan Najeriya cikin ɗan gajeren lokaci. Haka kuma, an yi ittifaqi a kan cewa basu da makawa, idan aka yi la’akari da yadda suka hana ci gaban tattalin arziƙi mai dorewa.

“Matsalolin da muke warwarewa babu shakka suna da fuskoki da yawa, masu alaƙa da juna, kuma suna da tushe mai zurfi, suna buƙatar ƙirƙira, dabaru, yanke shawara, da hanyoyi masu yawa wajen warware matsalolin. Waɗannan ƙaƙƙarfan matakai da ake aiwatarwa sun yi daidai da abin da ake buƙata.

“CBN ta kasance mai himma, ta ɓullo da wani tsari mai inganci don inganta hada-hadar kuɗi a kasuwar canjin kuɗi. Baya ga haɗe farashin, bankin ya kuma biya kuɗi mai yawa na bashin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, kuma ya zayyana sabbin hanyoyin gudanar da ayyukan bankunan kasuwanci, masu gudanar da ayyukan canji (BDC) da Masu Canjin Kudi na Duniya (IMTOs).

“Abin farin ciki ne a lura cewa mun fara ganin sakamakon. Lallai Naira yana daidaita, kuma kasuwar canjin kudi ta ƙasa tana samun ƙaruwar kuɗaɗen shiga. Alƙaluman baya-bayan nan na NBS sun nuna cewa shigo da kayayyaki zuwa Najeriya ya ƙaru da sama da kashi sittin da shida cikin ɗari a cikin rubu’i na huɗu na shakarar da ta gabata, idan aka kwatanta da rubu’in da ya gabata. Gwamnan Babban Bankin na CBN ya kuma bayyana yadda dalar Amurka biliyan ɗaya da dubu ɗari takwas ta shiga kasuwannin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje a makon da ya gabata, a kan sabbin sauye-sauyen da aka yi.

“Abin takaici, kamar yadda duk wani yunƙuri na yin sauye-sauye da tsaftace tsarin da ya samu gurin zama cikin ɓarna na dogon lokaci, ƙoƙarin na CBN ya gamu da tirjiya daga masu sayar da kuɗi a babban farashi da sauran ƴan wasa marasa kishin ƙasa a ciki da wajen ƙasarmu, waɗanda ke cin gajiyar tabarbarewar al’amura.

“Don magance wannan, hukumomin tsaro na gwamnati suna ta aiki ba dare ba rana a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, tare da haɗa ƙarfi da ƙarfe don magance waɗannan yunƙurin na lalata sauye-sauyen. Wannan ƙawancen ya haifar da ganowa, bincike, da takunkumi na mutane da ƙungiyoyin da ke da hannu cikin ayyukan da ba su dace ba da kuma zagon ƙasa a cikin kasuwar canji.

“An umurci jami’an tsaro da hukumomin tsaro da su sanya ido don ganin an kawar da munanan ayyukan da za su iya lalata kuɗin ƙasar mu, sannan kuma a hukunta waɗanda ke aikata waɗannan ayyukan. Gwamnati ba za ta bari a lalata ƙoƙarin ta ba.

Daidaiton darajar Naira don amfanin dukkan ‘yan Najeriya ne.

“Ya kamata ‘yan Najeriya su tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar wasu matakai na daidaita Naira da kuma kare tattalin arziƙin mu.

“Za mu ci gaba da neman haƙuri da fahimtar ‘yan Najeriya yayin da muke waɗannan lokuta masu wahala, zuwa lokacin fa’ida mai yawa da kuma sabon fata. Kamar yadda shugaban ƙasa yake jaddadawa, waɗannan ƙalubalen da muke fuskanta na wucin gadi ne kawai, kuma a dunƙule, tabbas za mu shawo kan su. 

“Shugaban ƙasa da tawagarsa za su ci gaba da jajircewa kuma za su mai da hankali kan aikin kawo ɗauki cikin gaggawa da kuma dawwamar wadata ga dukkan ‘yan Najeriya.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?