Back

Gwamnatin Tarayya za ta samar da ayyukan yi miliyan hamsin.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana shirin samar wa matasan Najeriya sama da miliyan hamsin ayyukan yi, a yayin da Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni ta kasa (CAC) ta ƙaddamar da rijistar ‘yan kasuwa miliyan biyu.

Ministar Masana’antu, Ciniki, da Zuba Jari, Dokta Doris Nkiruka Uzoka-Anite ce ta bayyana hakan a bikin ƙaddamar da fara aikin rajistar sabbin kamfanoni na haɗin gwiwa da Moniepoint don bunƙasa ɓangaren Ƙanana da Matsakaitan Kamfanoni (MSMEs), wanda za a gudanar da aikin a kan farashi mai rangwame don tabbatar da ci gaban tattalin arziƙin Najeriya.

Ministan ta bayyana shirin a matsayin wata gagarumar nasara da aka samu ta hanyar amfani da na’urorin sadarwa na zamani wajen haɓaka tattalin arziƙi.

Don haka ta ce samar da ayyukan yi don kawo sauyi ga tattalin arziƙin ƙasar nan na daga cikin abubuwa guda takwas da Shugaba Bola Tinubu yake son aiwatarwa da suka shafi samun damar kuɗi ga kowa da kowa, kawar da fatara, da ƙarfafa tattalin arziƙi.

Ministar ta bayyana shirye-shiryen gwamnati na ba da gudummawar da ake buƙata domin aikin, wanda shi ne irinsa na farko a tarihin ƙasar, Wanda Kuma alkiblar sa ce samar da ayyukan yi da samar da yanayin da za a iya bunƙasa harkokin kasuwanci.

Babban Magatakarda, kuma Shugaban Hukumar rajistar kamfanoni na CAC, Hussaini Ishaq Magaji, SAN, a lokacin taron wanda aka yi a Abuja, a na shi jawabin ya ce yin rijistar sabbin kamfanonin kasuwancin na daga cikin gudunmawar da Hukumar ta CAC ke bayarwa wajen tabbatar da shirin wannan gwamnatin na farfaɗo da tattalin arziƙi.

Don haka shugaban na CAC ya nuna jin daɗinsa kan  kan wannan haɗin kan wanda ya kara da cewa zai haifar ɗa mai idanu.

A nasa jawabin, Babban Jami’in Moniepoint, Babatunde Olofin, ya bayyana shirin su na aiwatar da aikin bisa tsarin gwamnati mai ci yanzu na farfaɗo da tattalin arziƙi.

Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a taron shi ne sarrafa akwatin Moniepoint wanda ke ɗauke da sabbin sana’o’i miliyan biyu da aka tsara. 

Idan za a tuna,  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada ƙudirinsa na farfaɗo da tattalin arziƙi a watan Nuwamba 2023 ta hanyar samar da ayyukan yi miliyan hamsin domin cika alƙawuran yaƙin neman zaɓensa.

An gudanar da taron a Bankin Masana’antu (BOI), wanda Ministan Masana’antu, Ciniki, da Zuba Jari, Dakta Doris Nkiruka Uzoka-Anite ta jagoranta, kamfanin harkokin kudi na Moniepoint. kuma ya ɗauki nauyin gudanarwa.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?