Back

Gwamnatin Tarayya zata gana da Dangote da BUA kan tsadar siminti

David Umahi, Ministan Ayyuka, ya yi kira da a yi taro da masu masana’antun siminti kan tashin farashi.

Farashin siminti ya yi ta kai-kawo tsakanin Naira dubu takwas zuwa Naira dubu goma Sha biyu kan kowanne buhu daga farashin shi na kimanin Naira dubu huɗu a makonnin da suka gabata.

Dangote, BUA, da Lafarge na daga cikin masu masana’antun da ma’aikatar ayyuka ta gayyace su.

Orji Uchenna Orji, mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, ya ce: “Damuwa da tsadar siminti duk da ɗimbin tallafin da ‘yan kwangilar gidaje da titina ke yi wa masana’antun siminti, Mai Girma Ministan Ayyuka, Sanata Injiniya Nweze David Umahi CON, ya gayyace taron gaggawa na duk masu masana’antun siminti a Najeriya”.

Orji ya ruwaito shugaban nasa yana cewa, bambamcin da ke tsakanin tsohon farashin masana’anta da farashin kasuwa yana da yawa.

“Sanin kowa ne cewa masana’antun suna da ƙalubalensu, waɗanda za mu yi nazari a kansu, amma daga binciken da muka yi, bambamcin da ke tsakanin tsohon farashin masana’anta da farashin kasuwa ya yi yawa,” in ji Umahi.

“Saboda haka ya kamata mu duba halin da ake ciki da sauran batutuwa da nufin samar da daidaiton farashin.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?