Back

Gwamnatin Tarayya zata samar da wadataccen abinci – Inji Bola Tinubu 

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin shi na kawo sauye-sauye a harkar noma domin ganin Najeriya ta dogara da kanta wajen samar da abinci da kuma fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa ƙasashen waje.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga Ƙungiyar Darikar Tijjaniyya ta Duniya ƙarƙashin jagorancin Khalifa Muhammad Mahe Niass a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Lahadi.

Hakan ya kasance kamar yadda ya ce gwamnatin shi za ta tallafa wa tsare-tsare da kuma ƙoƙarin bayar da sauƙi da taimako ga alhazai tare da jaddada ƙudirin gwamnatin tarayya na tallafawa ayyukan addini.

Shugaban ya bayyana buƙatar yin haɗin gwiwa tsakanin shugabannin siyasa da na addini don ci gaban muradun ƙasa da inganta haɗin kai a tsakanin jama’a.

“Najeriya za ta zama mai safarar fitar da abinci zuwa ƙasashen waje. Za a faɗaɗa samar da abinci sosai ta hanyar amfani da ingantattun injina wajen noma. Za mu kawo manyan motocin noma. Dole ne mu zama masu alkibla a matsayin mu na mutane. Wannan ita ce Sunna da ƙa’idojin da na fahimta tun lokacin da nake tasowa” inji shi.

Tinubu ya godewa Ƙungiyar Darikar Tijjaniyya ta Duniya bisa goyon baya da addu’o’i da suke yi, inda ya jaddada muhimmancin ƙoƙarin haɗin gwiwa wajen gina Najeriya ingantacciya.

A nasa ɓangaren, Sheikh Mahe Niass, Khalifan Tijjaniyya, wanda ya yi magana a madadin tawagar, ya yabawa shugaba Tinubu bisa jajircewar shi ta tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Nijeriya.

Tawagar ta gabatar da addu’o’in ci gaban ƙasa da na haɗin kai, da kuma na bukatar Allah ya ƙara wa Shugaba Tinubu hikima, ƙarfi da nasara wajen tafiyar da al’amuran ƙasar nan.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?