Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa babu wani ɗan jarida ɗaya da aka kama ko aka ɗaure a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu saboda gudanar da aikin jarida yadda ya kamata.
Ya jaddada cewa kafafen yaɗa labarai suna da cikakken ‘yanci a Nijeriya.
Idris ya faɗi haka ne a yayin da ya ke amsa wata tambaya a wani taron manema labarai da ma’aikatar sa ta shirya tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Kula Da Muhalli ta Tarayya da kuma Hukumar Ilimi da Kimiyya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), domin tunawa da Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya ta bana wanda aka yi a Abuja ranar Juma’a.
Ya ce: “A zamanin wannan gwamnatin, a misali, ban ga wani mutum wanda aka ɗaure ko kuma ya yi gudun hijira sakamakon ‘yancin aikin jarida ba.
“Mun san abin da ya faru a ƙasar nan a baya. A wasu shekarun da suka gabata, mun san cewa dole ne ku bar ƙasar nan don samun damar ba da rahoto. Zan iya gaya muku cewa ‘yan jarida a Nijeriya suna da ‘yanci amma za a iya ƙarfafa ‘yancin ne idan aka tabbatar da gaskiya ta hanyar da muke kawo rahoto.”
Ministan ya ce Shugaban Ƙasa Tinubu ya fahimci muhimmancin yaɗa labarai yadda ya kamata wajen wayar da kai, faɗakarwa, da ilimantar da ‘yan Nijeriya da duniya baki ɗaya, inda ya ƙara da cewa ta hanyar ba da sahihan bayanai a kan lokaci za a iya faɗakar da kowa sosai, kuma kafafen yaɗa labarai na iya zama makami mai ƙima na bunƙasa gaskiya da riƙon amana.
“A matsayin mu na Ma’aikata da Gwamnati, mun ba da dama ga ‘yan jarida ba tare da wata matsala ba kuma mun samar da yanayi mai dacewa wanda ya ci gaba da ƙarfafa wa kafafen yaɗa labarai na Nijeriya ƙwarin gwiwa don bunƙasa,” inji shi.
Ministan ya tunatar da kafafen yaɗa labarai cewa yaɗa labarin ƙarya bai dace da aikin jarida ba kuma ba za a iya kwatanta shi da ‘yancin jarida ba.
Ya ce yayin da Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin ganin Nijeriya ta zama wata ƙasa mai jan hankali wajen zuba jari kai-tsaye daga ƙasashen waje, dole ne kafafen yaɗa labarai su gabatar da kyakkyawan bayanin ƙasar ga ƙasashen duniya.
Yayin da ya ke magana kan taken Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya na bana, wato ”Jarida ta Duniya: Aikin Jarida a yayin da ake fuskantar Matsalar Muhalli,” Idris ya ce duniya na fuskantar matsalar muhalli mai girman gaske wanda ba a taɓa ganin irin sa ba, wanda ke haifar da barazana ba kawai ga duniya ba amma ga makomar bil’adama.
Ya ce sauyin yanayi, asarar rabe-raben halittu, gurɓacewar yanayi, da ƙarewar albarkatu munanan abubuwa ne da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa kan wayar da kan jama’a.
Ya ce, “Mu yi imani da cewa ‘yancin ‘yan jarida ba wai kawai haƙƙin ɗan’adam ba ne; ya na da muhimmanci don ɗorewar muhalli. Idan babu ‘yan jarida masu ‘yanci da zaman kan su, ba za mu iya fatan magance matsalolin muhalli da mu ke fuskanta ba.
“Yaɗa labaran ƙarya yana lalata fahimtar jama’a game da matsalolin muhalli kuma yana hana mu damar ɗaukar matakai masu ma’ana.
“Don haka dole ne mu tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancin ‘yan jarida tare da tallafa wa ayyukan ‘yan jarida masu sadaukar da kai wajen bayar da labarin gaskiya.”
Taron ya samu halartar Ƙaramin Ministan Kula da Muhalli, Dakta Iziaq Adekunle Salako; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Mista Bayo Onanuga; Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Watsa Labarai Da Wayar Da Kai, Dakta Ngozi Onwudiwe; Shugaban Ofishin UNESCO na Abuja, Mista Abdourahamane Diallo, da shugabannin hukumomin Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai da kuma Ma’aikatar Kula da Muhalli.