Back

Gwamnatin Tinubu tace zata iya rufe iyakokin ƙasar don magance ƙarancin abinci

Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta Shugaban kasa, Bola Tinubu ta ce tana tunanin yiwuwar sake rufe iyakokin ƙasar domin daƙile yawan fitar da kayayyaki da safarar abinci da ake yi ta haramtacciyar hanya.

Manufar Gwamnatin kamar yadda tayi bayani, ita ce samar da abinci ga ‘yan Najeriya.

Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Dattawa kan Harkokin Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin hada-hadar Kuɗi, da Tsare-tsare na Ƙasa kan ƙoƙarin da Gwamnatin ke yi na magance taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar, a ranar jumma’a da ta gabata.

Ministan ya ce duk da cewa gwamnati na yin duk abin da za ta iya domin rage tsadar kayan abinci, ya Kara da cewar babbar matsalar gwamnatin ita ce rashin ishashshen kariya da iyakokin kasar ke fama da shi, da Kuma yadda gwamnatin zata hana haramtaccen sufurin kayan abincin zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya wanda ya zama silar dake janyo wuyar samar da abinci ga al’umma.

Kyari ya ce: “Abin da muke fuskanta a yau shi ne fitar da abinci ba bisa ƙa’ida ba zuwa ƙasashen maƙwabta. A yau saifa ɗaya ta zama naira dubu biyu da naira hamsin, wato sefa dari ta zama Naira dubu biyu da dari biyu. Naira dari hudu ce sefa daya a shekarun baya.”

“Sefa ɗin nan kuɗi ne mai wuyar gaske, Idan ka kalli duk ƙasashe huɗu da ke maƙwabtaka da mu, abincin mu shi ne mafi arha a zagayen yankin saboda faɗuwar darajar Naira, .” Inji ministan 

“Don haka za ku ga ana fitar da kaya da yawa ba tare da takardar izini ba tare da yin fasa-kwauri ta kan iyakokin mu zuwa waɗannan ƙasashen maƙwabtan.”

“Bugu da ƙari, wani ɓangaren matsalar da muke da shi a tsawon wannan lokaci shi ne rashin samun kuɗin ƙasashen waje.”

“Masu zuba jari da dama, wato Indiyawa, Sinawa ko ‘Yan Turkiyya da suke gudanar da harkokin su a ƙasar nan, suna sayen amfanin gonakin mu da ake nema a waje, kamar waken suya da ridi, suna sayen su da tsada don kawai su samu kuɗaɗen waje. Daga nan sai su fitar da kayan domin su samu kuɗaɗen kasashen waje, kuma abin da ya fi muni shi ne yawancin waɗannan kuɗaɗen ba a maido da su ƙasar mu.”

“Fitar da kayayyaki abu ne mai kyau a gare mu, amma idan ba ku sami kuɗin waje ba kuma ba a dawo mana da shi ba kuma gwamnati ba ta samun kuɗin shiga daga wannan harkar, babbar illa ce ga ƙasar baki daya.”

“Don haka abin da muke ƙoƙarin yi a nan shi ne muna ƙoƙarin haɓaka samar da kayayyaki, musamman na abinci.’

“Ina ganin batu ne na tattalin arziƙi tsakanin samarwa da buƙata, amma abin takaici, dole ne mu ga yadda za mu iya samar da abincin ga ‘yan ƙasarmu miliyan dari biyu da talatin, kuma a lokaci guda. Idan aka ci gaba da wannan yanayin na tattalin arziƙi, to dole ne a rufe iyakoki wanda ya saɓawa ƙa’idar kungiyar haɗin kan Afirka ECOWAS ko kuma samarwa ɗaukacin yammacin Afirka kayan abincin.”

Yace “Wannan abin takaici ne, amma idan za mu iya tsare filin ƙasar mu da kuma sa manoma su koma gona, na tabbata za mu iya yin hakan.”

“Muna da hekta miliyan 70 na fili a Najeriya. Don haka waɗannan ƙalubale ne da muka tsinci kanmu a ciki, amma ina farin cikin nan ba da jimawa ba za mu fara aiki a tsakanin kwanaki takwas zuwa 10 masu zuwa, tare da taimakon Shugaban Ƙasa da kuma Mai Kula da Harkokin Tattalin Arziƙi, muna son tallafa wa manoma don noman rani.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?