Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) tare da tallafin Shirin Duniya na Daidaiton Rigakafi na ƙasar Canada (CANGive), ta haɗa hannu da Gwamnatin Jihar Yobe domin yiwa ‘yan mata 350,000 masu shekaru 9 zuwa 14 allurar rigakafin cutar kansar mahaifa a faɗin ƙananan hukumomi 17 na jihar.
An ƙaddamar da shirin rigakafin cutar HPV (Human Papillomavirus) a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Damaturu.
An gano HPV a matsayin babban abu mai haɗari a cikin kashi 95% na cututtukan kansar mahaifa.
Dakta Alhassan Hamisu Dama, Ko’odinetan Ofishin Hukumar ta WHO a Jihar Yobe, ya ce Hukumar za ta kashe sama da dala 50,000 domin tallafawa Jihar Yobe wajen gudanar da aikin cikin nasara.
Ya bayyana cewa tawagogin makarantu da na al’umma 365 za su yi wa ‘yan mata allurar rigakafi a makarantu da kuma sansanonin da ba sa zuwa makaranta nan da kwanaki biyar masu zuwa.
Dakta Dama ya ce cutar kansar mahaifa ita ce ta biyu da ke haifar da yawan mace-macen mata masu shekaru 15 zuwa 19 a Nijeriya, wanda ke haifar da sabbin kamuwa da cutar 12,075 a duk shekara a duniya.
Dakta Babagana Kundi Machina, Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Yobe, ya bayyana cewa jihar za ta yi amfani da tawagogi 565 da aka girke a cibiyoyin lafiya, makarantu, da kuma al’ummomi.