Back

Gwamnatin Zamfara ta ƙaryata haramta sarrafa burodi, ta ce, toshe hanyoyin samar wa ne ga ‘yan bindiga ne kawai

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ba ta hana sarrafa biredi ba a kowane yanki na jihar.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa matakin da gwamnati ta ɗauka ya shafi hana samar da kayayyaki ne kawai ga ‘yan bindigar a faɗin jihar.

Wannan bayanin na zuwa ne bayan da Ƙungiyar Masu Yin Burodi a Jihar Zamfara ta bayar da umarnin dakatar da sarrafa biredi saboda dokar da gwamnati ta yi na hana babura rarraba burodi a cikin Jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a Gusau, ta bayyana cewa an aiwatar da dokar hana samar da burodi da man fetur ga yankunan da ba su da zaman lafiya domin daƙile ayyukan ‘yan bindiga da ke addabar jihar.

“Gwamnatin jihar Zamfara ba ta da niyyar yin katsalandan a harkar sarrafawa ko kuma sayar da biredi, wanda abinci ne mai muhimmanci a gidaje da dama.

“Bugu da ƙari, muna son jaddada cewa gwamnatin mu ta himmatu wajen tallafawa kasuwancin cikin gida da kuma tabbatar da cewa duk ‘yan jiha za su iya samun abinci mai muhimmanci.

“Mun fahimci muhimmiyar rawar da ƙananan ‘yan kasuwa ke takawa a cikin tattalin arziƙin jihar mu, kuma mun himmatu wajen samar da yanayin da za su ci gaba.

“Mun tsara wani shiri na daƙile hare-haren ‘yan bindigar, da haifar da ruɗani a wasu sassan jihar.”

Idris ya ƙara da cewa dabarar gwamnati ta haɗa da hana samar da burodi da man fetur ga yankunan da ba su da zaman lafiya don daƙile ayyukan ‘yan bindigar, saboda suna dogaro da waɗannan muhimman abubuwa don aiwatar da ayyukansu na laifi.

Wannan matakin, a cewar shi, wani babban shiri ne na maido da zaman lafiya da tsaro a yankunan da abin ya shafa da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Gwamnati ta tabbatar wa mazauna yankin da masu kasuwanci cewa jita-jitar da ke haifar da ruɗani da damuwa ba gaskiya ba ce, ta ƙara da cewa ta ci gaba da jajircewa wajen samar da yanayin da za a samu ci gaba a harkokin kasuwanci a jihar Zamfara.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?