Back

Gwamnatin Zamfara ta biya garatuti na N2.3bn ga masu ritaya 1,746

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ta biya sama da naira biliyan 2.3 a matsayin garatuti ga ma’aikatan gwamnati 1,746 da suka yi ritaya a jihar.

Sulaiman Idris, Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Dauda Lawal kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau.

Idris ya bayyana cewa adadin waɗanda suka yi ritaya 1,746 na jiha da na ƙananan hukumomi a jihar sun karɓi sama da naira biliyan 2.3.

Ya ce: “Mun tantance ma’aikata 3,079 da suka yi ritaya a ƙoƙarin da ake yi na biyan garatuti da ake bin gwamnatocin baya.

“Tuni aka fara biyan kaso na biyu na garatutin ‘yan fansho waɗanda aka tantance a ranar Juma’a, 1 ga Maris.

“Jimillar ma’aikata 413 da aka tabbatar sun yi ritaya daga aikin gwamnati an biya su naira miliyan 682.2.”

Idris ya ci gaba da cewa an kuma fara biyan kaso na biyu na waɗanda suka yi ritaya daga aiki a ƙananan hukumomi.

“An biya ‘yan fansho 403 da aka tantance daga ƙananan hukumomin waɗanda adadin kuɗin su ya kai naira miliyan 449.6,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?