Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da dakatar da sayar da man fetur a Jarkoki ko galan na wani dan lokaci ga masu ababen hawa a gidajen mai.
Haka Kuma Gwamnatin ta dakatar da sayarwa ko rarraba burodi kan babura masu kafafu uku, ko biyu a duk fadin jihar.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron kwamitin tsaro na jihar da aka gudanar a gidan gwamnati a karshen mako, kwamishinan yada labarai da al’adu, Mannir Muazu Haidara ya ce majalisar ta dauki matakin ne sakamakon munanan ayyukan da wasu gidajen man da suka fara Al’adar sayar da man fetur a Jarkoki da burodi ga wadanda ake zargin ‘yan fashi ne da makami a wasu kauyukan jihar.
A cewar Kwamishinan sayar da man fetur a Jarka da burodi da ake sayarwa wasu da ake zargin zargin ‘yan fashi ne ya yi kamari sosai a kusan daukacin al’ummar jihar ta Zamfara, kuma gwamnati ba za ta ci gaba da kallon wadannan munanan ayyuka ba don haka ya shawarci wadanda abin ya shafa da su bi wannan dokar.
Kwamishinan ya bukaci Wadanda ke yin badakalar da su daina wannan aika-aika, daga yanzu. Yana kira ga jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu da laifin karya wannan dokar.
Hakazalika, a wani bangare na alkawurran sake tunkarar kalubalen tsaro da ke addabar jihar, Kwamishina Haidara ya ci gaba da bayyana cewa, an hana like gilashin mota da bakaken leda, rufe lambar mota da Kuma hawa mota ana jiniya da wasu ke yi ba tare da an basu izini ba.
majalisar ta kuma umurci jami’an tsaro da su kama duk Wanda ya karya dokar, su kuma gurfanar da su a gaban shari’a