Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun gana da Majalisar Ɗinkin Duniya kan taimakon jin ƙai da kuma dawo da zaman lafiya a yankinsu.
Jihohin Arewa maso Yamma da dama dai sun fuskanci matsalar ‘yan bindinga da ta’addanci a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ya janyo wa al’ummar yankin ƙuncin rayuwa.
Wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Ƙasa na Cibiyar Watsa Labarai ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNIC), Oluseyi Soremekun, ya fitar a ranar Juma’a, ta bayyana cewa gwamnonin yankin Arewa maso Yamma na Nijeriya sun gana da tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya ƙarƙashin jagorancin mai kula da ayyukan jin ƙai, Mohamed Malick Fall, kuma sun buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya da ta tallafa wa jihohinsu domin tunkarar matsalolin ci gaba da dama da suke fuskanta.
Sanarwar ta ce: “Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma kuma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranci sauran gwamnonin yankin da suka haɗa da Sanata Uba Sani na Jihar Kaduna; Abba Kabir Yusuf na Kano; Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi; Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir; da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zuwa Gidan Majalisar Ɗinkin Duniya dake Abuja.
“Gwamnonin sun bayyana manyan ƙalubalen da yankin ke fuskanta, da suka haɗa da rashin tsaro, talauci, yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, da yawaitar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, yawan mace-macen yara da mata masu juna biyu, da ɗimbin matasa da ba su da aikin yi.
“Sun nuna cewa kusan kashi 80 cikin 100 na al’ummar suna samun abin rayuwarsu ne ta hanyar noma, duk da haka, suna fuskantar ƙalubalen gurbacewar ƙasa da kuma sauyin yanayi, wanda hakan ya jawo raguwar amfanin gonakinsu. Gwamnonin sun kuma yi tsokaci kan yadda yara ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.”
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma a cikin sanarwar ya ce: “Ya kamata mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙi da talauci da rashin aikin yi, kasancewar manyan abubuwan da ke haddasa rashin tsaro a yankin.”
A nasa ɓangaren, Kodinetan Majalisar Ɗinkin Duniya, ya bayyana jin daɗinsa da karɓar gwamnonin shida daga cikin bakwai na shiyyar. Ya ba da tabbacin cewa Majalisar Ɗinkin Duniya za ta tallafa wa yankin Arewa maso Yamma don magance matsalolin ci gaba.