Back

Gwanatin Tarayya Ta Ba da Dalilan Da Suka Sa Za A Bayar Da Lamunin Ɗalibai Kai Tsaye Ga Jami’oi 

Sakataren zartarwa na asusun ba da lamunin ilimi na Najeriya, Akin Sawyerr ya ce za a bayar da lamunin dalibai kai tsaye ga cibiyoyi masu bayar da ilimi na gaba da sakandare domin kaucewa karkatar da Kuɗaɗen.

Ya kuma yi nuni da cewa, za a ba wa Ɗalibai da suka samu lamunin shekaru biyu bayan sun kammala aikin yi wa kasa hidima na tilas kafin su biya bashin.

Sawyerr ya bayyana haka ne a wata ganawa da babban sakataren hukumar kula da jami’o’in kasar nan, Chris Maiyaki a Abuja.

Kamar yadda muka samu wani rahoton taron da aka yi a Abuja, Sawyer ya bayyana cewa, hanyoyin da gwamnati za ta samu kudaden bayar da lamunin sun hada da, kashi daya cikin dari na duk ribar da Gwamnatin Tarayya ke samu daga sayar da man fetur da sauran ma’adanai.

Wasu hanyoyin kuma sune, kashi daya bisa dari na haraji da ake samu daga Hukumar Haraji ta Tarayya, Hukumar Shigi da Fici ta Najeriya, Hukumar Kwastam ta Najeriya, da wasu hanyoyin na Ƙididdigar Ilimi da Tsare-tsaren Asusun Ilimi.

Ya kuma bayyana cewa, za a bayar da lamunin ilimi ta hanyar Karbar gudummuwa, kyaututtuka da kuma kudaden shiga da ke shigowa daga wasu hanyoyi.

A halin da ake ciki, malaman da ke karkashin kungiyar malaman jami’o’i, reshen Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure, sun sake jaddada kin amincewa da shirin bayar da lamunin daliban da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta kaddamar.

Malaman sun bayyana shirin a matsayin wata hanya ta hana kudaden da jami’o’in gwamnati ke samu, inda suka ce idan aka aiwatar da shirin, zai kara dagula al’amuran daliban Najeriya marasa galihu.

Shugaban kungiyar ASUU na FUTA Farfesa Pius Mogaji ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayar da kyautar tallafin karatu ga wasu hazikan daliban makarantar a ranar Juma’a.

Mogaji ya bayyana cewa shirin da aka tsara zai sa dalibai su ci bashi na dindindin, inda ya kara da cewa zai sa jami’o’in gwamnati su fuskanci rashin kudaden daga gwamnati

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?