Back

Hajji: Gwamnatin Jigawa ta bada tallafin naira miliyan ɗaya ga kowane maniyyaci

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da tallafin naira miliyan ɗaya ga kowane maniyyaci dake jihar domin aikin hajjin bana.

Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

A cewarsa, gwamnan ya ɗauki matakin ne biyo bayan ƙarin kuɗin aikin Hajji da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta yi.

“Akwai mutanen da suka rigaya sun biya kuɗinsu, amma kwatsam sai aka samu ƙarin kuɗin aikin Hajji, ƙarin kuɗin Hajji babban ƙalubale ne ga ɗimbin maniyyata,” inji Labbo.

Ya kuma buƙaci maniyyatan jihar da su tabbatar sun biya sauran kuɗaɗen da suka rage na sama da naira dubu ɗari tara da goma sha takwas ga hukumar.

Babban Daraktan ya yi nuni da cewa waɗanda za su ci gajiyar tallafin aikin Hajji su ne waɗanda suka rigaya sun biya wani bangare na kuɗin ga hukumar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?