Gwamnatin jihar Kebbi ta ba kowane maniyyaci da ke son zuwa aikin hajjin bana daga jihar tallafin naira miliyan 1 don kammala biyan ƙarin kuɗin tafiya na kimanin naira miliyan biyu da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar.
An cimma wannan matsaya ne a taron Majalisar Zartarwa na Gaggawa wanda Mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Umar Abubakar Tafida ya jagoranta, a Birnin Kebbi ranar Litinin.
Da yake ƙarin haske ga manema labarai game da sakamakon taron, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Alhaji Yakubu Ahmad Birnin Kebbi, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin bunƙasa karamcin Gwamna Nasir Idris na ganin an kiyaye addini domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.
Ya bayyana cewa an tsara kuɗin da aka baiwa kowane maniyyaci ne domin a samu sauƙin biyan kuɗin tafiyan gaba ɗaya kafin ranar rufewa.
“A cikin kimanin naira miliyan 2 da NAHCON ta nema a matsayin ƙarin kuɗin tafiya, gwamnatin jihar Kebbi ta biya wa kowane maniyyaci naira miliyan 1 yayin da maniyyata za su biya sauran don kammala kuɗin tafiyar su.
“Maniyyatan da suka kammala biyan kuɗin suma za su amfana da karamcin naira miliyan ɗaya daga hannun gwamnati,” inji kwamishinan.
Dangane da kutsen da wasu ɓata-gari suka yi a wasu ma’ajiyoyin abinci da nufin wawushe hatsi, Alhaji Yakubu Ahmad Birnin Kebbi, ya sanar da kafa wani kwamiti mai mutane 13 a ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Noma domin gudanar da bincike kan lamarin, wanda gwamnati ta bayyana a matsayin abinda ya cancanci ayi Allah-wadai dashi.