Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), ta ƙulla yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama na Max Air da Air Peace domin jigilar alhazan 2024 zuwa da kuma daga ƙasar Saudiyya.
Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Arabi, wanda ya jagoranci aikin a Gidan Hajji da ke Abuja, ya buƙaci kamfanonin jiragen sama da su ba da fifiko kan tsaro da jin daɗin alhazai.
Ya ce aikin jiragen sama wajen samun nasarar aikin Hajji yana muhimmanci sosai.
“Ku manyan masu ruwa da tsaki ne, ku abokan ci gaba ne kuma kun san yawan abin da ake tsammani daga gare mu duka.
“Wannan ba shine karon farko da zaku ɗauki wannan babban nauyi ba amma har yanzu ana tsammanin samun nasarar fita waje.
“NAHCON za ta ƙulla yarjejeniya da ku amma yawancin abin da ake tsammani ya dogara ne akan amana.
“Ina so in tunatar da ku cewa kuna da suna da zaku kare, duk abin da kuka yi wanda ke da kyau zai wuce ku. NAHCON ba ta da shakku a ranta cewa za ku yi nasara.”
Ya kuma jaddada buƙatar kamfanonin jiragen sama su ɗauki tsaron alhazai da muhimmanci.
Tun da farko, Kwamishinan Ayyuka na NAHCON, Mista Anofi Elegushi, ya ce ƙulla yarjejeniyar ya nuna wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali da lumana.
“Ƙulla yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama, shaida ce ta jajircewarmu na samar da ingantacciyar hidima ga maniyyatanmu.
“Yayin da muke ci gaba da aiwatar da wannan yarjejeniya, ina da yaƙinin cewa haɗin gwiwar da muke yi da kamfanonin jiragen sama zai haifar da masaniya mai kyau da tasiri ga maniyyatan mu.”