Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ki amincewa da bukatar wani mawaki mazaunin Kano, Abdul Kamal, na bukatar kotun tayi amfani da karfin ta, ta dakatar da Sashen Hausa na gidan rediyon Birtaniya BBC daina amfani da kidan da mallakin shi ne ba tare da izinin shi ba.
Kotun ta ce tunda tana da damar ta bayar da izini ko kuma ta dakatar da kafafen yada labarai amfani da sautin, sai ta ce neman Hana amfani da sautin na wucin gadi da mawakinn ke bukata ba shi da wani inganci. A maimakon haka, sai kotun ta ba da umarnin a gaggauta sauraron karar.
Aminiya ta ruwaito cewa Kamal ya kai karar Sashen Hausa na BBC ne saboda amfani da wakar shi ta sauti a cikin shahararren shirin su na “Daga Bakin Mai ita,” ba tare da izinin shi ba.
Lauyan wadanda ake kara, Barista Shakiruddeen Mobuluwaji, ya shaidawa kotun cewa har yanzu lauyan wanda ya shigar da karar bai amsa karar da aka shigar ba.
Lauyan wanda ya shigar da karar, Barista Bashir Ibrahim, ya ce tuni ya mika wa lauyoyin wadanda ake karar da martanin da suka dace akan lokaci.
Alkalin kotun, Mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa, ya bukaci bangarorin da ke shari’ar da su tabbatar da mayar da martani sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar ashirn ga watan uku na wannan shekarar.