Lokaci ya shuɗe da masu karatun digiri na farko a jami’o’i ke komawa aji da kuɗi da sauran kayan aikin gida waɗanda ke nuna kyakkyawan yanayin rayuwarsu a cikin Makarantun su.
A yau da yawa iyaye ko masu kula da ‘yan’yan riko ba za su iya samun rayuwa mai sauki ba, ballanta ta iso ga ’ya’yan na su, ko ‘yanyan riƙon na su.
An gano cewa ɗalibai a manyan makarantun yanzu suna sayar da wasu kayan aikin gida da na’urori don ciyar da kansu, a lokacin mawuyacin hali da aka shiga a halin yanzu a cikin ƙasar.
A cewar wani ɗalibi Mai suna Murtala Gsrba,, ya bayyana cewa suna sayen waɗannan na’urori ne a lokacin da suke da arha, ta hanyar amfani da kuɗaɗen da iyayen su, suka ba su domin amfani dasu, yayin da waɗanda ke da na’urorin ke sayar da su a lokacin da suke buƙatar kuɗi don biyan buƙatu da Kuma abinci.
Ya ce: “Abin ban takaici ne ganin ’ɗanuwanka ɗalibi yana shan wahala don samun abinci, ya samu tsira a cikin wannan mawuyacin halin tattalin arziƙi.
“Tattalin arziƙin ƙasa yayi munanana ga iyayen mu da masu kula da mu, don haka yake shafar mu.
“A da wasu abokan kwanan mu a ɗakin kwanan daliɓai suna zuwa da buhunan kayan abinci da sauran na’urori masu amfani da ke taimaka wa mana wajen shaƙatawa amma yanzu saboda farashin abinci ya ruɓanya ya kara, an daina samun irin wannan yanayin.
“Masu kasuwancin da ke kusa da makarantu, su ma ba sa taimakawa al’amuran, ga tsawwalawa ga rashin taimakawa, sai su ƙara farashin kaya da zarar ɗalibi ne ke sayen su.
“Da yawa daga cikin mu a yanzu dole ne mu yi amfani da kuɗaɗen da ba su da wani amfani ta hanyar siyan kayan gida da na’urori da aka yi amfani dasu kamar gado, firji, kati, silindar gas, talabijin da sauran abubuwa daga ɗaliban da suka kammala karatun.
“A yanzu ana yin gwanjon waɗannan abubuwa akan wasu shahararrun dandamalin kasuwancin yanar gizo da ɗalibai suka sani.
“Amma wasu ɗaliban da suka kawo waɗannan na’urori daga gida suna sayar da su a lokacin buƙata a farashi mai sauƙi.”
Miss. Lovet Momoh, ɗaliba ‘yar matakin 200 ta ce tana fatan samun kyakkyawan yanayin rayuwa tun matakin 100 a makaranta. Amma mutuwar mahaifinta tare da yanayin tattalin arziƙi ya ruguza burinta.
“Lokacin da na sami admission a ƙarshen 2022 na yi farin ciki da imani cewa zan rayu kamar gimbiya a makaranta.
“Sai na rasa mahaifina sannan ƙanin mahaifiyata ya ɗauki nauyin karatuna.
“Ban taɓa tunanin abubuwa za su yi wahala kamar wannan ba. Ba zan iya kiransa don ƙananan buƙatu ba saboda abun kunya ne a wurina sosai.
“Sai na ga abokaina suna siyan kayan da aka yi amfani da su a wajen ɗaliban da suka kammala karatu suna gwanjonsu a tsakiyar shekaran karatun su.
Da na tambaye su sai suka koya mun.
“Nima na fara siyan kayan da aka yi amfani da su da wasu kuɗin aljihuna sannan na sayar da su a kan farashi mai tsada a yanar gizo.”
“Kamar yadda muka sani, farashin kayayyaki da na ayyuka na ƙaruwa, haka ma na kayan da aka yi amfani da su. Wannan ita ce hanyar rayuwata a da da kuma yanzu yayin da nake makaranta.