
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda zai cika shekaru 72 a ranar Juma’a, 29 ga Maris, 2024, ya ce baya son wani taron bikin ranar haihuwarsa.
A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, ya fitar a madadinsa, Tinubu ya ce ranar za ta kasance wani muhimmin ci gaba a rayuwarsa a matsayinsa na shugaba kuma dattijon ƙasa.
Ya ce don girmama lokutan da ake fuskantar ƙalubale, ba zai ɗauki nauyin gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwa ba, kuma ba ya son wani daga cikin abokansa da masu fatan alheri a faɗin ƙasar nan ya shirya duk wani taron biki a madadinsa ko da sunan sa.
“A yayin wani gagarumin biki kamar wannan, ya zama al’ada ga ’yan uwa, abokai da abokan tarayya su yi bikinsa ta hanyoyi daban-daban.
“Shugaba Tinubu ya yaba da girmamawar kasancewarsa jagoran ƙasa mafi girma a Afirka a wannan lokaci kuma yana aiki tuƙuru don kyautata rayuwa ga al’ummarmu baƙi daya.
“A cewarsa, saboda halin da al’ummar ƙasar ke ciki a baya-bayan nan da kuma kashe jami’an sojoji da ‘yan sandan mu a jihar Delta da kuma yadda wasu ’yan ta’adda ke tafka ta’asa a sassan Nijeriya a baya-bayan nan, bai kamata a yi wani taron zagayowar ranar haihuwa da kuma sanya saƙonnin talla na fatan alheri a jaridu ba. Kada a sanya saƙonnin fatan alheri a gidajen rediyo da talabijin ma.
“Shugaba Tinubu ya umurci abokai da abokan hulɗar da ke son sanya tallace-tallacen fatan alheri da su ba da gudummawar kuɗaɗen ga ƙungiyoyin agaji da suke so da sunan sa. Duk da cewa Shugaban Ƙasa ya yaba da irin ƙarfin halin sojojin mu wajen kuɓutar da ‘ya’yanmu da aka yi garkuwa da su a Kuriga da jihar Kaduna da kuma jihar Sakkwato, zai yi amfani da damar ranar haihuwarsa wajen yin tunani tare da sake sadaukar da kan sa wajen samar da Nijeriya daidaitacciya, mai tsaro, mai wadata da kuma mai haɗin kai.”