Back

Har yanzu gwamnatin tarayya na biyan Naira tiriliyan daya kan tallafin mai a duk wata – Shugaban Kamfanin Mai na Pinnacle

Babban jami’in gudanarwa, CEO kuma manajan darakta na kamfanin Pinnacle Oil and Gas Limited, Robert Dickerman, ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin Najeriya na biyan naira tiriliyan daya a duk wata domin tallafin man fetur.

Hakan dai na faruwa ne duk da cire wasu dokoki na man fetur kamar yadda shugaba Bola Tinubu ya sanar a ranar rantsar da shi.

Kamfanin mai na Pinnacle ya ce yanzu haka Najeriya na kashe kusan Naira tiriliyan daya a duk wata wajen biyan tallafin man fetur.

Dickerman ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake halartar wani taron tattaunawa a wani zama na shida na Nigeria’s Downstream Forum, taron da aka kammala kwanan nan na makamashin Najeriya (NIES) a Abuja.

Ya kara da cewa har yanzu akwai gagarumin tallafi, inda ya kara da cewa hakan ya taimaka wajen samar da farashin mai mai araha da kuma kara rura wutar ayyukan fasa kwaurin mai zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

Ya ce, “Masu zuba jari na kasashen waje, masu ba da lamuni na kasashen waje da DFIs da gwamnati ke gudanarwa sun fito fili a kan abin da suke so ya tabbata na manufofin kasafin kudi, magance cin hanci da rashawa, ba da damar gasar kasuwanci, da tabbatar da adalci a kasuwanni ta hanyar manufofi, tsari da kuma ikon aiwatar da kwangila.” 

“Ina so in nuna cewa har yanzu akwai tallafi Mai yawa dangane da man fetur, duk da cewa wannan a cikin wani sashin na farashin ne, ba farashin daloli ba kamar yadda yake a duniya.”

“Sakamakon wannan tallafin shine, samun farashin man fetur mafi sauki a Najeriya cikin nahiyar Afirka, wanda ke karfafa fasakwaurin man yana kuma kara ragewa Najeriya darajar man”

“Tsarin fasahohin na janyowa Najeriya tallafin kasashen da ke makwabtaka da ita ko da a lokacin da tattalin arzikin mu ke tabarbarewa ne. 

Tsarin yana yin illa ga kasafin kudin na gwamnatin tarayya gaba ɗaya, da na Jihohin ta, saboda ba za a iya aiwatar da ayyuka masu mahimmanci ba dalilin biyan wannan tallafin. A halin yanzu ana lissafin kusan Naira tiriliyan daya a kowane wata.

“Har ila yau, da wannan tallafin da aka dakatar da biya zai haifar da rashin samar da mai idan babu matatun mai da ke samar da mai a ƙasar.

“Dukkanin wadu kayayyaki da ake amfani da su suna zuwa ne daga kasuwannin duniya wanda za a sayar da su ne kawai a farashin da kasuwa ta bayar.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?