Shugaban Hukumar Kula da Aikin Injiniya a Nijeriya (COREN), Farfesa Sadiq Abubakar, ya ce hauhawar farashin siminti da ake yi ba bisa ƙa’ida ba ne ke haddasa rugujewar gine-gine a ƙasar.
Ya bayyana hakan ne a zaman binciken Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Wakilai kan Ma’adanai, Masana’antu, Kasuwanci da Ayyuka na Musamman na Majalisar Wakilai kan ƙarin farashin a ranar Litinin.
A cewarsa, ƙarin farashin ya haifar da raguwar ingancin gine-gine a ƙasar.
Ya ce, “Za ku yarda da ni, wannan yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suke haddasa rugujewar gine-gine. Ina ƙoƙarin alaƙanta ƙarin farashin siminti tare da ingancin gine-ginen mu da rushewar gine-gine. A bayyane yake, akwai alaƙa da hakan kuma ina ganin wannan abu ne da ya kamata mu yi tambayoyi akai.”
Da yake jawabi, Shugaban Kwamitin, Ɗan Majalisa Jonathan Gaza Gbwefi Gbewfi, ya amince da Shugaban COREN kan iƙirarinsa cewa farashin siminti yana da alaƙa kai tsaye da rushewar gine-gine da kuma alaƙa kai tsaye da ƙarin farashin haya.
Shugaban kwamitin ya zargi Ƙungiyar Masu Sana’ar Siminti ta Nijeriya da yin amfani da umarnin kotu wajen kawo cikas ga bincike kan hauhawar farashin siminti a ƙasar.
Hakan ya biyo bayan rashin bayyanar shugaban ƙungiyar a gaban kwamitin bayan gayyata har sau biyu.