
Ɗalibai mutane biyu ne na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi, da ke garin Lokoja suka rasa rayukan su bayan shaƙar hayaƙin janareta da aka ajiye kusa da tagar dakin su cikin dare.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, SP William Ovye Aya ne ya tabbatar da hakan a wata hira da yayi da ‘yan Jaridu ta wayar tarho a ranar alhamis da ta gabata.
SP, Aya, ya bayyana cewa waɗanda suka mutun sun haɗa da Bilikisu Eleojo, ‘yar shekara ashirin, da kuma Ibrahim Halliru.
A cewar sa, an ajiye janaretan ne a kusa da tagar waɗanda abin ya shafa, inda suka yi barci suna shaƙar hayakin har ya toshe masu hanyoyin numfashi suka rasa rayukan su kafin gari ya waye.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu maƙwabta ne suka gano gawarwakin ɗalibam guda biyu a ɗakin tun da sanyin safiyar Alhamis.
“Akwai ɗalibai uku daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi a cikin ɗakin. Ɗaya Bilikisu Tijani Eleojo, mai shekaru 20, Ibrahim Haliru, da Mercy Ojochegbe.”
“Bilikisu Tijani Eleojo, da Ibrahim Haliru sun riga sun rasu a lokacin da maƙwabta suka gano lamarin da safiyar ranar alhamis yayin da Mercy Ojochegbe ke numfashi aka kuma garzaya da ita asibiti.
“An kai rahoton lamarin ga rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, a garin Lokoja kuma ana ci gaba da bincike.” inji Kakakin ‘yan Sandan
‘Yan Sandan sun gargaɗi mazauna garin da su kasance masu kiyaye lafiya a koda yaushe domin gujewa gubar hayaƙi a gidajensu.
A watan Disamba, wani matashi da budurwar sa suma sun rayukan su bayan da aka ruwaito sun shaƙi hayaƙi daga wani janareta da aka kulle a cikin ɗakin su cikin dare a unguwar Ugborikoko, ƙaramar hukumar Uvwie ta jihar Delta.
An tattaro cewa mutumin ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar budurwar sa a wani gidan rawa.
An tattaro cewa da barin wajen liyafar, sai suka je shagon matar, suka sanya injin din samar da wutar lantarki a ciki kafin su yi barci, kuma suka rasu kafin gari ya waye.