Back

Hedikwatar Tsaro na neman ɗan Nijar da laifin ta’addanci, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, da sauransu

Hedikwatar Tsaro (DHQ) a ranar Alhamis ta bayyana cewa tana neman wani ɗan Nijar, Halilu Buzu, ruwa a jallo bisa zargin ta’addanci, safarar bindigogi, satar shanu da kuma haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a Zamfara.

Rundunar sojin ta zargi Buzu da hannu wajen kashe mutanen ƙauye 19 a Farar Ƙasa da ke Zamfara.

Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya bayyana cewa Halilu babban mai sayar da makamai ne kuma dillalan makamai sun amince da shi don samar da makamai daga Libya.

A cewarsa, lokacin da sojoji suka kusa kai masa hari, sai ya tsallaka kan iyakar Jamhuriyar Nijar domin samun mafaka.

Janar Buba ya buƙaci hukumomin Nijar da su kama shi su miƙa shi ga Nijeriya.

Ya ce: “Sojoji suna farautar wani mai suna HALILU BUZU, shugaban ‘yan ta’adda da ya fito daga Buzu a Jamhuriyar Nijar. Ya zauna a dajin Subbubu kuma yana zaune a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara.

“Sasanin sa da wurin da yake haƙo ma’adinin zinare ba bisa ƙa’ida ba suna Kawayi a ƙaramar hukumar Anka ta Jihar Zamfara, inda yake da yara maza da dama da suke yi masa aiki.

“Halilu kuma fitaccen ɓarawon shanu ne kuma mai haƙo zinari ba bisa ƙa’ida ba. A makon da ya gabata, yaran sa sun kashe mutanen ƙauye 19 a Farar Kasa. A halin yanzu, yana ɗaya daga cikin wasu da dama da za mu ayyana ana nema.

“Bugu da ƙari, Halilu babban mai sayar da makamai ne, wanda dillalan makamai suka amince da shi don samar da makamai daga Libya. Lokacin da sojoji suka kusa kai masa hari, sai ya zarce kan iyakar Jamhuriyar Nijar don neman mafaka. A wannan lokaci, muna kira ga hukumomin Nijar ta hanyoyin da suka dace da su kama shi tare da hukunta shi kan wannan ta’asa da ya yi.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?