Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa aƙalla mutane 97 ake nema ruwa a jallo.
Mutanen da ake neman ruwa a jallo sun haɗa da ‘yan bindiga da ‘yan tada ƙayar baya, da dai sauransu, waɗanda ke da hannu wajen aikata munanan laifuka a ƙasar.
Sun kuma haɗa da shugaban masu fafutukar kafa ƙasar Biafra, Simon Ekpa.
Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya tabbatar da sunaye da hotunan mutanen da suka bayyana cewa suna nema ruwa a jallo a ranar Juma’a.
Ba kamar a watan Nuwambar 2022 ba, lokacin da sojoji suka bayyana cewa aƙalla shugabannin ‘yan bindiga 19 ne ake nema ruwa a jallo da ladar naira miliyan 5 a kan kowannen su domin ƙarfafa gwiwar ‘yan Nijeriya su bayar da bayanan da za su kai ga kama su, a wannan karon, ba wani tukuici da aka sanya kan mutanen 97 da aka bayyana ana nema ruwa a jallo.
Sunaye da hotunan sun ƙunshi ‘yan tada ƙayar baya daga Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da kuma masu tada ƙayar baya a yankin Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.
Kimanin mutane 43 ne aka sanar ana nema ruwa a jallo a shiyyar Arewa maso Yamma da rikicin ‘yan bindiga ya lalata, daga cikinsu akwai:
Alhaji Shingi; Malindi Yakubu; Boka; Dogo Gide; Halilu Sububu; Ado Aliero; Bello Turji; Dan Bokkolo; Labi Yadi; Nagala; Saidu Idris; Kachalla Rugga, da Sani Gurgu.
A yankin Arewa maso Gabas da rikicin Boko Haram da ƙungiyar ISWAP mai da’awar jihadi a yammacin Afirka suka lalata, an sanar da cewa mutane 33 ne ake nema ruwa a jallo.
Daga cikinsu akwai Abu Zaida; Modu Sulum; Baba Data; Ahmad; Sani Teacher; Baa Sadiq; Abdul Saad; Kaka Abi; Mohammed Khalifa; Umar Tella; Abu Mutahid; Mallam Muhammad; Mallam Tahiru Baga; Uzaiya, da Ali Ngule.
Har ila yau, an sanar da cewa ana neman ‘yan tada ƙayar baya 21 da ‘yan ta’adda a yankin Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.
Su ne Simon Ekpa; Chika Edoziem; Egede; Zuma ; ThankGod; Gentle; Flavour ; Mathew; David Ndubuisi ; High Chief Williams Agbor; Ebuka Nwaka; Friday Ojimka; Obiemesi Chukwudi aka Dan Chuk ; David Ezekwem Chidiebube, da Amobi Chinonso Okafor wanda aka sani da Temple da sauransu.