Back

Hedikwatar Tsaro ta gargaɗi fararen hula kan kai wa jami’an soji hari

Hedikwatar Tsaro (DHQ) a ranar Alhamis ta gargaɗi fararen hula game da hare-haren da suke kaiwa kan jami’anta, tana mai cewa “lamarin yana da mummunan tasiri ga ƙwarin gwiwar sojoji.”

Gargaɗin ya biyo bayan abubuwan da suka faru ne a Banex Plaza da ke Abuja inda fararen hula suka kai hari kan jami’an soji da ba su ɗauke da makamai da kuma Okuama a Jihar Delta inda aka kashe sojoji 17 da ke aikin samar da zaman lafiya.

Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya yi gargaɗin cewa ba za a sake lamuntar irin waɗannan hare-hare ba.

Ya ƙara da cewa, kashe-kashen ba gaira ba dalili da aka yi wa jami’ai 17 a Okuama da ke Jihar Delta, tare da harin da aka kai a Banex Plaza da ke Abuja a kwanan nan, abin takaici ne.

A cewarsa, waɗannan abubuwan da suka faru ba su da kyau ga tsaron ƙasarmu, ba su da fa’ida kuma zaluntar kai ne.

Buba ya gargaɗi fararen hula da su kula da maganganunsu da ayyukansu, wanda zai iya yin tasiri ga aikin sojoji.

Ya ce: “Haƙiƙa, bai kamata a yi wa ɗan adam haka ba, musamman jami’an soji da ke kare ’yan ƙasa ko kuma su tsare ƙasar.”

Ya bayyana cewa don cin nasarar wannan yaƙin, “muna buƙatar goyon bayan mutane. Muna kuma fatan jama’a su gane cewa suna buƙatar sojoji su ci nasara a yaƙin don tabbatar da tsaron lafiyarsu.

“Saboda haka, wannan bai kamata ya sake maimaita kansa ba domin yana kawo cikas ga muradunmu duka. Idan sojoji sun yi kuskure, a kai rahoto kuma tsarin shari’ar soja zai magance lamarin. Muna cikin yaƙi, kuma dole ne ‘yan ƙasa su gane cewa suma suna da alhaki ta hanyar ayyukansu da maganganunsu na tallafawa sojoji don kiyaye ƙwarin gwiwa da kuzarin yaƙi na sojoji a koyaushe.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?