Back

Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi watsi da jita-jitar juyin mulki

Hedkwatar tsaron Najeriya a yau ranar Litinin ta karyata zargin da wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa cewa an sanya rundunar tsaro (Guards Brigade) a fadar shugaban kasa cikin shirin ko-ta-kwana bayan wasu zarge-zargen da ake yi na sa Idon wasu akan kujerar mulkin ƙasar, lamarin da ke nuna fargabar yunkurin juyin mulki.

A wata sanarwa da mukaddashin Daraktan yada labarai na rundunar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ya ce, “An jawo hankalin hedkwatar tsaro kan wani labari na karya da wata jarida ta buga a yanar gizo a ranar ishirin da biyar ga wannan watan tana mai cewa an sanya masu tsaro cikin shirin ko-ta-kwana biyo bayan wani motsi da ba a saba gani ba a fadar Shugaban kasa, wanda ya kai ga zargin yunkurin juyin mulki a Najeriya.”

“Jaridar ta kuma bayyana a cikin wasu abubuwa cewa zargin ya haifar da taron gaggawa da ya hada da shugaban kasa Bola Tinubu, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da kuma kwamandan rundunar soji.”

“Hedikwatar tsaro na son bayyanawa a fili cewa zargin karya ne.

“Domin kaucewa shakku, an dora wa rundunar tsaro alhakin kare kujerar mulkin Fadar Shugaban kasa bisa doka da kuma kara tsaro ga Babban Birnin Tarayya da kewaye.”

“Saboda haka, ya kamata a lura cewa, a ko da yaushe rundunar Guards Brigade ta kasance cikin shirin ko ta kwana domin gudanar da ayyukan da aka dora mata yadda ya kamata.

“Idan za a iya tunawa, babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, a wasu tarurruka daban-daban, ya nanata kudirin rundunar sojojin Nijeriya ba tare da bata lokaci ba, na tabbatar da kariya da dorewar dimokradiyya a Nijeriya.

Ya ce, Saboda haka, hedkwatar tsaro ta yi Allah wadai da wannan ikirari mara tushe wanda hasashe ne kawai na mawallafin kuma ya umarci jama’a da su yi watsi da shi.

“Bugu da kari, hedkwatar tsaro ta yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gaggauta daukar matakin da ya dace a kan Sahara Reporters kan wannan mataki na rashin kishin kasa.

“A halin da ake ciki, hedkwatar tsaro za ta nemi hakkin doka kan lamarin wanda ke da wata manufa ta haifar da tashin hankalin a cikin kasar.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?