Wani jirgin sama mai saukar ungulu ɗauke da Shugaban Ƙasar Iran, Ebrahim Raisi, ya yi hatsari yayin da yake ziyara a Gabashin Azarbaijan, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim ya ruwaito a ranar Lahadi.
Lamarin dai ya faru ne a cikin yanayi mai cike da hazo, wanda ya zuwa yanzu ya hana ma’aikatan gaggawa isa wurin jirgin.
“Mai girma Shugaban Ƙasa da ayarinsa na kan hanyarsu ta komawa cikin wasu jirage masu saukar ungulu, kuma ɗaya daga cikin jirage masu saukar ungulu ya sauka ƙasa babu shiri saboda rashin kyawun yanayi da hazo,” inji Ministan Harkokin Cikin Gida, Ahmad Vahidi, a wani sharhi da aka watsa a gidan talabijin na ƙasar.
“Tawagar ceto daban-daban na kan hanyarsu ta zuwa yankin, amma saboda rashin kyawun yanayi da hazo, zai iya ɗaukar lokaci kafin su isa jirgin.”
Ya ƙara da cewa, “Yana da wuya a tuntuɓe su. Muna jiran ƙungiyoyin ceto su isa wurin da jirgin ya sauka kuma su ba mu ƙarin bayani.”
Fasinjojin da ke cikin jirgin sun haɗa da Shugaban Ƙasa Raisi; Limamin Tabriz, Ayatullah Al Hashem; da Ministan Harkokin Wajen Ƙasar, Hossein Amir Abdollahian; da Gwamnan Gabashin Azarbaijan, Malik Rahmati, da wasu jami’ai da dama.