Back

Hisbah Ta Kama Shahararriyar ‘Yar TikTok A Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama fitacciyar ‘yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya bisa zargin aikata lalata.

Aliyu Usman, shugaban rundunar ‘Operation ‘Kai da badala’ wanda ke rike da mukamin jami’in sa ido, shi ya tabbatar da wannan kamun.

Ya ce, “An kama ta ne jiya (Litinin) da yamma a gidanta da ke unguwar Tinshama. “Kusan awa uku muka yi muna jiran ta kafin daga bisani ta fito muka damke ta.”

“Ana tuhumarta da aikata lalata da aka santa da ita. Akwai wanda kullum yake zuwa ya dauke ta da misalin karfe goma na dare ya dawo da ita da karfe goma sha biyu na dare ko karfe daya na safe.” inji shi 

Ya kara da cewa za a gurfanar da Kunya a gaban kotun shari’ah da ke zama a PRP ranar Talata.

Hukumar Hisbah ta kaddamar da farautar akalla mashahuran ’yan Tiktok guda shida da ake zargi da yada bidiyoyi na batanci a shafukan sada zumunta.

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan watanni da babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya gayyaci daukacin mata ‘yan Tiktok da ke Kano zuwa wani zama inda hukumar ta yi tayin gyarawa da karfafa musu sana’o’i da tallafin karatu.

A wajen taron, Sheikh Daurawa ya hori daukacin ‘yan Tiktok da sauran masu sha’awar shafukan sada zumunta da su daina yada abubuwan da za su iya karfafa lalata a cikin al’umma.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?