
Ɗaliban Kuriga da aka ceto.
‘Yan makaranta 137 da aka sace daga Kuriga, ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, waɗanda aka sako ranar Lahadi, sun isa gidan gwamnati da ke Kaduna.
A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sakin yaran a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun gwamnan jihar, Uba Sani.
Duba hotunan yaran a ƙasa: