Back

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya ta bayyana Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagles

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta bayyana Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagles a sakatariyar ta da ke Abuja ranar Litinin.

Ministan Wasanni na Nijeriya, John Enoh; Shugaban NFF, Ibrahim Gusau; da Babban Sakataren Hukumar Ƙwallon Ƙafa, Mohammed Sanusi, na daga cikin manyan baƙin da suka halarci bikin ƙaddamarwar.

Tsohon ɗan wasan Ajax da Real Betis ya kasance mataimaki ga tsohon mai kula da tawagar, Jose Peseiro na tsawon watanni 20.

Ya riƙe Super Eagles a matsayin kocin riƙo a wasan sada zumunci da Ghana da Mali a watan Maris.

Finidi zai jagoranci wasansa na farko a hukumance da Bafana Bafana na Afirka ta Kudu a watan gobe.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?