
Finidi George
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya a ranar Litinin ta amince da naɗin tsohon ɗan wasan gaba, Finidi George, a matsayin Babban Kocin Tawagar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles.
George, wanda ya shafe watanni 20 a matsayin mataimaki ga José Santos Peseiro kafin ɗan ƙasar Portugal ɗin ya bar muƙamin da raɗin kansa bayan da tawagar ta zo a matsayi na biyu a Gasar Cin Kofin Afrika a Cote d’Ivoire 2023, ya jagoranci tawagar a matsayin wucin gadi a wasanni biyu na sada zumunci a Morocco a watan jiya.
Tawagarsa ta doke Ghana da ci 2-1 a wasan farko, inda suka kawo ƙarshen shekaru 18 ba tare da samun nasara ba a kan Black Stars, amma sai suka sha kashi a hannun Mali da ci 0-2 a wasa na biyu.
George, wanda ɗan ƙungiyar ‘Golden Generation’ ne da ta lashe gasar cin kofin ƙasashen Afrika a shekarar 1994 a Tunisia, kuma ta zama tawaga ta biyu mafi nishaɗantarwa a wasan farko da Nijeriya ta buga a Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA da aka yi a Amurka a wannan shekarar, ya lashe wasanni 62 wa Nijeriya, ciki har da wasan ƙarshe na gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA a 1994 da 1998. Ya kuma lashe ƙarfen zinare da azurfa da tagulla daga gasar AFCON a shekarun 1992 da 1994 da 2000 da 2002.
Tsohon ɗan wasan Ajax Amsterdam (Netherlands) da Real Betis (Spain) mai shekaru 52, wanda ya fara zura ƙwallo a raga a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika da Burkina Faso a filin wasa na ƙasa, Legas ranar 27 ga Yuli 1991, ya kuma yi fice a Calabar Rovers da Sharks FC a cikin gida kafin ya tafi Turai. Ya taimaka wa Rashidi Yekini wajen zura wa Nijeriya ƙwallo ta farko a gasar cin kofin duniya ta FIFA da Bulgaria a Dallas, Amurka a ranar 19 ga Yuni 1994.h
George ya zura ƙwallon da ta kai Nijeriya a gasar cin kofin duniya ta FIFA na farko, lokacin da ya sanya Nijeriya a gaba da Algeria a wasan share fage a Algiers a ranar 8 ga Oktoba 1993. Wasan ya ƙare da ci 1-1 kuma Nijeriya ta samu tikitin zuwa wasan ƙarshe a Amurka.
Aikin George yanzu shi ne jagorantar Super Eagles zuwa ga nasara a wasanni biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 da Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Benin a Uyo da Abidjan bi da bi, a cikin ‘yan sama da makonni biyar. Wasan ya zama tilas ne a yi nasara, tunda Super Eagles ke matsayi na uku a rukunin C na gasar cin kofin Afirka bayan Rwanda da Afirka ta Kudu.