Back

Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta yi jigilar maniyyata 10,675 zuwa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta yi jigilar maniyyata 10,675 zuwa ƙasar Saudiyya domin aikin hajjin 2024.

Wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Hajiya Fatima Usara ta fitar, ta ce FlyNas ta yi jigilar maniyyata 4,665, sai Max Air da 4,479 yayin da Air Peace ta kai maniyyata 1,531 a cikin kwanaki shida na aikin.

Hukumar ta ce kawo yanzu, ba a samu labarin soke jirgi ba sai dai jinkirin da jirgin ya yi wanda ya haifar da tsaikon lokaci da ya shafi jirgin na farko na Kwara; canza shi daga 20 ga Mayu, 2024 zuwa farkon sa’o’in Talata, 21 ga Mayu.

NAHCON ta ce Jihar Nasarawa ce ta fara kammala jigilar maniyyata ta jirgin sama da ya kai 1,794 a lokacin aikin hajjin shekarar 2024.

Ana sa ran Jihar Oyo da Sojoji za su kammala jigilar maniyyatan su a daren ranar Talata.

Hukumar ta ci gaba da cewa: “Yayin da muke kusan mako na biyu na jigilar maniyyata zuwa Saudiyya, jihohin da za su fara jigilar maniyyatan su sun haɗa da jihohin Kaduna, Yobe, Kano, Adamawa, Borno da Sokoto. A yau ma maniyyatan Jihar Filato za su tashi.

“An shawarci maniyyata da su kwantar da hankalinsu kuma su lura cewa Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) tana da tsarin Farkon Shiga Farkon Fita (FIFO) ma’ana dawowa daga Saudi Arabiya zuwa Nijeriya zai bi tsarin tashi daga Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya. Don haka, ana sa ran dukkan maniyyata za su yi adadin kwanaki a Masarautar daidai lokacin isar da su.”

A wani labarin kuma, NAHCON ta ce an shawo kan ƙalubalen da aka fara fuskanta a fannin bayar da Allawus na Balaguro (BTA) ga maniyyatan. A yanzu kowanne maniyyaci yana da dala 500 a matsayin BTA kamar yadda NAHCON ta amince da shi a madadin katin kiredit.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?