Back

Hukumar alhazai ta Kaduna ta rasa darakta

Marigayiya Hajiya Hannatu Zailani

Daraktar Kuɗi da Gudanarwa na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, Hajiya Hannatu Zailani ta rasu.

Ta rasu ne a ranar Asabar a wani asibiti mai zaman kansa dake Kaduna bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Alhaji Yunusa Mohammed Abdullahi ya sanya wa hannu, ya bayyana marigayiyar a matsayin “ma’aikaciya mai ƙwazo a hukumar.”

Ta fara aikinta ne a farkon shekarun 1990 kuma ta samu matsayi da dama har ta kai ga zama Daraktar Kuɗi da Gudanarwa. Daga 2019 zuwa 2022, ta kuma yi aiki a matsayin mai kula da hukumar.

Ya ce: “Za a yi matuƙar kewar ƙwazo da shugabancin Hajiya Hannatu. Muna miƙa ta’aziyyarmu ga ‘yan uwa, abokanta, da abokan aikinta.”

Marigayiyar ta bar mijinta da ‘ya’yanta.

An yi jana’izar ta ne a ranar Asabar a maƙabartar Unguwar Sarki Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inji Jami’in Hulɗa da Jama’a.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?