Back

Hukumar Alhazai ta Kaduna za ta fara jigilar maniyyata a ranar 23 ga Mayu

Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa za a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa ƙasar Saudiyya daga ranar 23 ga watan Mayun 2024.

Ta ce kamfanin jirgin sama na Max Air ne zai yi jigilar maniyyatan jihar zuwa ƙasa mai tsarki a bana.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Yunusa Muhammad Abdullahi ya fitar, ya ce an sanya ranar ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), hukumar jiha, da kuma wakilan kamfanin jirgin.

Idan dai ba a manta ba a watan Nuwamban da ya gabata ne Gwamna Uba Sani ya kafa kwamitin da zai kula da ayyukan Hajji da kuma tabbatar da jin daɗin alhazai.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, shugaban kwamitin, Malam Salihu S. Abubakar, wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai, ya gana da shugabannin sassan maniyyatan.

A wajen taron, ya jaddada ƙudirin kwamitin na tabbatar da gudanar da aikin Hajji ba tare da tangarda ba, inda ya buƙaci shugabannin sassan da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na jagoranci da kuma kare haƙƙoƙin maniyyata.

Malam Abubakar ya kuma shawarci maniyyata da su ci gaba da hulɗa da jami’ai, sannan ya kuma gargaɗe su da su yi hattara da masu damfara, kamar yadda ya bayyana fatan samun nasarar aikin hajjin.

Maniyyata 4,776 daga jihar da suka kammala biyan dukkan kuɗaɗen da ake buƙata a lokacin da aka ƙayyade za su yi aikin Hajjin bana.

Waɗannan maniyyata ne da suka cika wa’adin da NAHCON ta bayar na biyan kuɗaɗen a ranar 12 ga Fabrairu, 2024 ko kuma kafin ranar 12 ga watan Fabrairu na naira miliyan 4.5 da kuma ƙarin N1,199,000.

Waɗanda suka cika wannan wa’adin sun cancanci samun tallafin Gwamnatin Tarayya kuma an ba su damar biyan ƙarin naira miliyan 1.9 a ko kafin ranar 28 ga Maris, amma waɗannan maniyyatan sun iya biyan kuɗin da aka ƙayyade zuwa ranar 17 ga Maris.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?