Back

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta kayyade farashin karshe kan aikin hajjin bana.

A farkon watan goma na shekarar da ta wuce ne hukumar Alhazan Najeriya ta bayyana kudin da aka fara biya na zuwa aikin hajjin bana Naira miliyan hudu da dubu dari biyar (N4.5m) inda ta ce adadin kudin ya kasance “daidai ne da farashin dala da zata tantance farashin karshe na aikin Hajji mai zuwa”, kuma adadin zai baiwa hukumar haƙiƙanin yin ciniki na farashin masauki, kuɗin jirgin sama, ciyarwa, da sauran abubuwan buƙatu.

Sai dai a wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakiyar daraktan hulda da jama’a ta hukumar NAHCON, Fatima Usara, da ta rabawa manema labarai a ranar Asabar, hukumar ta ce ta yi kokarin kula da farashin a kan naira militan hudu da rabi (N4.5m,) amma sai da ta yi gyara saboda “tabarbarewar dala domin ta samu daidaita da darajar musayar kudi.”

Usara ta kara da cewa, yayin da shugaban hukumar, Jalal Arabi, ya tattauna kan farashin da masu samar da hidima a kasar Saudiyya a makon da ya gabata ya sa a yi gyare-gyaren farashin, inda ya ce kudin zai kai Naira miliyan shida idan ba ayi gyara ba.

“Za a iya tunawa da farko, Shugaban Hukumar Alhazan, Malam Jalal Ahmad Arabi ya yi niyyar kula da aikin Hajjin bana kan Naira miliyan hudu da rabi da aka karba a matsayin kudin ajiya na farko. Hasashen ya kasance mai girma har sai da aka samu faduwar darajar Naira.

“Abin takaici, rashin kwanciyar hankali da aka samu a farashin dala a baya-bayan nan ya tilasta yin gyare-gyaren da ya dace duk da irin kokarin da Shugaban Hukumar aikin hajjin ya yi na kula da farashin aikin Hajjin bana a kan wannan adadin”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?