Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa (DRTS) a cikin Babban Birnin Tarayya, ta ce Tawagar Ta na Musamman ta kama motoci 1,408, babura na kasuwanci 3,712 da adaidaita sahu 1,112 tsakanin Janairu zuwa Disamba 2023 a cikin yankin.
Hakan na ƙunshe ne a cikin ƙididdigar da DRTS ta fitar a ranar Laraba ga Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) a Abuja ta hannun Shugaban ta na Hulɗa da Jama’a da Wayar da Kai, Mista Kalu Emetu.
Bisa ƙididdigar da aka yi, an lalata babura 3,712 na kasuwanci da aka kama, yayin da aka sako wasu daga cikin motocin ga masu su bayan an biya tara da gyararrakin da aka yi musu.
Ya ce hukumar ta samu sama da naira miliyan 127.541 a shekarar 2023 daga tarar da masu motocin da adaidaita sahun da aka kama suka biya a cikin asusun gwamnati.
Emetu ya bayyana cewa, motocin da aka kama waɗanda ba su dace a tuƙa su ba, yawanci ana mayar dasu tarkace ne ana miƙa su ga masu su, don a hana tuƙa su.
Ya bayyana cewa lalata baburan da motocin ya yi daidai da dokar Babban Birnin Tarayya na hana baburan kasuwanci da motoci waɗanda basu cancanta ba a cikin birnin.
Kakakin ya ƙara da cewa bisa ƙa’ida, duk baburan da aka kama saboda karya dokokin hanya, sun zama na gwamnati kai tsaye.
Ƙididdiga na alƙalumman ya nuna cewa an kama motoci 217, babura na kasuwanci 836, da adaidaita sahu 298 a tsakanin Janairu da Maris 2023 a duk faɗin FCT.
Hukumar ta DRTS ta kuma kame motoci 270, babura 964, da adaidaita sahu 268 a cikin kwata na biyu na shekarar da ake nazari a kai, yayin da aka kama motoci 482, babura 931, da adaidaita sahu 353 aka kama daga watan Yuli zuwa Satumba.
A cikin kwata na ƙarshe na shekarar, bayanan DRTS sun nuna cewa an kama motoci 425, babura na kasuwanci 832 da adaidaita sahu 186 a yankin bisa laifuka daban-daban.