
A jiya ne Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shiga fafatukar kawo ƙarshen faɗuwar darajar Naira.
Hukumar ta ƙaddamar da murƙushe masu aikata haramtacciyar harkar kuɗi, da kamfanonin da ke ba da lissafin kaya a kuɗaɗen kasashen waje.
Hukumar ta EFCCn ta ce ta kafa rundunaoni na musamman har guda goma Sha hudu domin kamo masu laifin.
Hukumar, wacce ta sanar da kama wasu masu aikata haramtacciyar harkar kuɗi da dama a Legas, Fatakwal da Kaduna, ta ce kowace rundunar za ta yi aiki ne daga ƙananan hukumomin goma Sha hudu na hukumar.
Haka kuma ta gayyaci wasu mamallakan jami’o’i masu zaman kansu da sauran manyan makarantu waɗanda ke karɓar kudin dalibai kan daloli domin ta yi musu tambayoyi.
Wannan ci gaban ya zo ne a ranar da Ƙungiyar ‘Yan Kasuwan Canji Ta Najeriya, ABCON ta buƙaci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bar mambobin ta su dawo da sayar da dala.
A jiya ne dai Naira ta sauya farashi akan N1,490/$ a kasuwan bayan fage da kuma N1,418/$ a bankuna.
A cikin wata sanarwa da Shugaban yada labarai na hukumar ya fitar, Mista Dele Oyewale yace, jami’an da ke aiki za su “tabbatar da aiwatar da wasu dokoki game da la’antar kuɗin ƙasa da amfani da dala maimakon Naira.”
“Tawagar, wadda Shugaban Hukumar, Ola Olukoyede, ya ƙaddamar, an samar da ita ne domin kare tattalin arziƙin ƙasa Najeriya daga cin zarafi, da tawaye wanda zai kara taɓarɓarewar tattalin arziki”
Hukumar EFFC tace “Ana shawartar jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ya saɓa wa tanadin wannan doka ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da Babban Bankin Najeriya (CBN) domin ɗaukar matakin da ya dace.”
Ko da yake Hukumar ta EFCC ta yi shiru kan adadin waɗanda aka kama, ta ce wasu da ake zargin ana yi musu tambayoyi.