Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), ta ce ba ta ɗaukar ma’aikata a halin yanzu, kuma ta gargaɗi masu neman aiki da kada su faɗa hannun ‘yan damfara.
Jami’in Ilimantar da Jama’a na Hukumar (CPEO), Mataimakin Shugaban Hukumar Mista Jonas Agwu, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadi a Abuja.
Agwu ya ce bayanin ya zama dole ne biyo bayan ƙoƙarin da wasu da ake zargin ‘yan damfara ne su damfari masu neman aiki ko masu ɗaukar nauyinsu.
Ya ce an jawo hankalin rundunar ga wata kafar yaɗa labarai ta yanar gizo, inda ta yi wa jama’a bayanin yadda ake ci gaba da ɗaukar ma’aikata a ayyukan hukumar.
“Ana sanar da jama’a cewa hukumar ba ta ɗaukar ma’aikata a halin yanzu haka kuma babu wani shiri da ake yi don hakan.
“Shugaban Hukumar FRSC, Dauda Ali-Biu, yana so ya gargaɗi masu neman shiga ayyukan hukumar, da sauran jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya da yaudara
“Ana gargaɗin jama’a da su daina duk wani hulɗa tare da ‘yan damfarar da masu yaɗa wancan labarin ƙaryan saboda Hukumar ba za ta zama abin zargi ba idan aka damfari wani,” inji shi.