Back

Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ta yi watsi da jerin sunayen da ake yaɗawa na ‘yan sandan da aka ɗauka aiki

Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) ta yi watsi da jerin sunayen waɗanda aka ɗauka aiki a matsayin jami’an ‘Yan Sandan Nijeriya da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta.

Mista Ikechukwu Ani, Jami’in Hulɗa da Jama’a na PSC ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

“Hukumar ta yi watsi da jerin sunayen da ke yawo a wasu wuraren da ba na hukuma ba a matsayin sunayen waɗanda suka yi nasara a ɗaukar ma’aikata da aka kammala,” inji shi.

Ya ce hukumar na kuma sane da wata sanarwar manema labarai da aka ce ta fito daga Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar kan jerin sunayen waɗanda suka yi nasara wanda tuni hukumar ta yi watsi da shi.

“Duk da haka, hukumar na son bayar da umarnin Rundunar ‘Yan Sanda ta binciki inda aka samu labarin ƙaryar tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin,” inji Ani.

A cewarsa, Hukumar Ɗaukar Ma’aikatan ta Haɗin Gwiwa ita ce kawai hukumar da kundin tsarin mulki ya ba ta ikon ɗaukar jami’an ‘Yan Sandan Nijeriya.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?