Back

Hukumar Kwastam ta Apapa Tana Samun fiye da Naira Biliyan goma Sha Shida A Kullum 

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sashen Apapa ta bayyana a jiya cewa ta samar da kudaden shiga biliyan sha shida da miliyan ashirin da daya da dubu dari shida da sittin da dari hudu da sha biyu (N16,021,660,412).

Wannan adadi shi ne mafi girman kudaden shiga na yau da kullun a tarihin hukumar wanda ya haura Naira biliyan goma Sha daya da miliyan uku da aka tara a ranar ashirn da biuu ga watan sha dayan bara, da kuma Naira biliyan goma a ranar uku ga watan takwas na shekarar da ta wuce.

Shugaban yankin, Babajide Jaiyeoba ne ya bayyana wannan nasarar a matsayin daya daga cikin abubuwan da ake sa ran za ta samu daga cikin dabaru da dama da ya sanya a gaba, ya kuma bukaci jami’an rundunar da su ci gaba da jajircewa wajen ganin sun co gaba da wannan aikin bisa doka da kuma tabbatar da Babu ja da baya wajen kan duk wani abu da ya saba wa doka ta Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCSA) 2023.

Wannan, in ji shi, abin yabawa ne ta hanyar tattara kudaden shiga ta fuskar raguwar yawan kasuwancin da aka samu, kuma hakan ya samu ne sakamakon tarurrukan dabarun mako-mako tsakanin hukumar rajistar kamfanoni CAC da shugabannin sassan don yin nazari da tantance nasara da kalubalen ci gaba da inganta nasarorin da rundunar ta samu.

Bincike ya nuna cewa an sha samun hada-hadar masu ruwa da tsaki a kai-a-kai tsakanin hukumomin gwamnati, masu shigo da kaya, masu fitar da kayayyaki, masu gudanar da ayyukan tasha, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar cire kaya da samar da kayayyaki domin cimma burin da aka sa gaba.

Ya ce, Masu ruwa da tsakin sun ce an samu gagarumin ci gaba a yawan kwantenan da ake tantancewa a hukumar domin a rage bata lokaci tare da gudanar da aiki daidai da abin da hukumar kwastam ta zamani ta gindaya.

Yayin da yake yaba wa jami’an rundunar bisa sadaukarwar da suka yi wajen aiki a kan lokaci da rikon amana.

Jaiyeoba ya bukaci masu shigo da kaya da jami’an kwastam masu lasisi da masu jigilar kaya da su kara rungumar yin scanning kamar yadda hukumar kwastam karkashin kwanturola janar CGC Bashir Adewale Adeniyi, ta himmatu wajen ayyuka bisa yanar gizo domin sauƙaƙe ciniki.

A cewar shi, rashin yin furuci na gaskiya shine ke dakile harkay kasuwanci da ke iya haifar da jinkiri, wanda kuma ke hana fa’idodin jin daɗin tafiya cikin sauri.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?