Hukumar kwatsam ta Najeriya ta fara sayar da kayan abincin da ta kama wadanda aka biyo da su ta hanyar haram a duk yankunan da take da ma’aikata a cikin fadin ƙasar a yau jumma’a.
Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Adewale Adeniyi, a ranar alhamis ya ce za a fara rabon kayan abincin da aka kama a yau Juma’a.
Adeniyi, yayin da yake zantawa da manema labarai, ya yi gargadin cewa kada a mayar da kayayyakin abincin ya zamo kayan sari.
Ya kuma yi gargadin cewa an haramtawa jami’an kwastam siyan wannan kayayyakin, inda ya kara da cewa za a sayar da shinkafar a cikin buhu mai kilogiram ashirin da biyar akan kudi Naira dubu goma.
Idan ba a manta ba Hukumar kwastam ta ce za ta kammala shirin fara rabon kayayyakin abincin da aka kama ga ‘yan Najeriya kai tsaye.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Maiwada ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Da yake bayar da karin haske kan ka’idojin, Adeniyi ya ce, dole ne wadanda suka cancanta su ba da lambar tantancewa ta Najeriya (NIN).
Kamar yadda ya ce, Kungiyoyin da ke hari domin cin moriyar sayar da shinkafar sun hada da masu sana’ar hannu, malamai, ma’aikatan jinya, kungiyoyin addini, da sauran ‘yan Najeriya a yankunan da hukumar ke gudanar da ayyukan ta.
“Manufar mu ita ce mu gudanar da wannan aikin ta hanyar kungiyoyi irin wadannan Kai tsaye kai tsaye domin tabbatar da tasirin wannan aikin.”
Ya kuma yi gargadi kan cin riba ko cin gajiyar shirin.
Ya ce, Ya zama wajibi wadanda suka ci gajiyar wannan aikin su fahimci cewa ba za su sake siyar da wannan kayan ba a matsayin siye da siyarwa domin cin riba.
“Mun dauki matakai masu tsauri a kan duk wani nau’i na cin riba ko cin gajiyar wannan shiri. Muna kira ga ’yan Najeriya da su kai rahoton duk wanda ya karya ka’ida ko kuma ya sake sayar da kayayyakin abincin da aka kama ba tare da izini ba,” inji shi
Ya ci gaba da cewa hukumar ta himmatu wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin wannan tsari.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen daukar kwakkwaran mataki kan duk wani mutum ko wata hukuma da aka samu da saba ka’idojin wannan shiri,” in ji.
Adeniyi ya ce nau’in sayar da shinkafar ba dauwamamme bane, zai kasance ne wata hanya da hukumar za ta kwashe kayayyakin abincin da aka kama a halin yanzu.
“Mun zo nan ne domin mu ba da haske kan kudurin hukumar na kare al’ummar mu ta hanyar tabbatar da wadatar kayan abinci masu mahimmanci. A cikin ‘yan watannin nan, gwamnati na magance matsalolin da ake fuskanta a cikin tattalin arzikin mu.
“Fitar da Kayayyakin ake yi da yawa zuwa kasashen makwabta. Wasu daga cikin kayayyakin sun hada da, fiye da buhuna dubu biyu na hatsi iri-iri, kwali dubu biyu da buhunan kifi dari tara da sittin na busasshen kifi.
“Wasu kuma busasshen barkono ne, tumatir, man girki, macaroni, gishiri, sukari, garri. Wannan abin ba za a bari ya dore ba saboda yana sanya matsi da tsadar abinci, kuma yana yin barazana ga lafiyar mu,” in ji Adeniyi.