Hukumar Kwastam ta Tsibirin Tin-Can ta Nijeriya ta kama wasu makamai da alburusai da ake zargin wasu gungun miyagu ne suka shigo da su ƙasar ta ɓarauniyar hanya.
Daga cikin abubuwan da aka kama sun haɗa da rigunan sojoji, bindigogi, da miyagun ƙwayoyi irin su tabar wiwi.
Ko da yake, har yanzu ana kan zayyana cikakkun bayanai game da katsewar, majiyoyi sun ce an ƙwato makaman ne a yayin da ake duba kayayyakin da aka shigo da su ƙasar.
Kawo yanzu dai ba a bayyana ko an kama wani ba.
Daƙilewar na zuwa ne bayan wata takwas da hukumar kwastam ta kama makamai iri-iri 31 a tashar Tin-Can da Multi-Purpose Terminals (PTML) da ke Legas.
Kwanturolan hukumar ta Kwastam, Mista Adewale Adeniyi, ya shaidawa manema labarai a lokacin cewa an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannun su.
Cikakkun bayanai daga baya…