Hukumar Kwastam ta Najeriya NCS, reshen jihar Kano, ta cafke wasu manyan motoci guda hudu na kayan abinci a wani mataki na magance matsalar fasa kwauri.
A cikin sanarwar da kakakin hukumar, Saidu Nuradeen, ya fitar a yau Talata a Kano, ya bayyana cewa jami’an hukumar sun kama motoci masu jigilar kayayyaki masu yawa da aka yi niyyar fitarwa ba bisa ka’ida ba a kan titin Hadejia zuwa Taura zuwa Ringim a Jihar Jigawa.
Kakakin, ya jera kayayyakin da aka kama wadanda suka hada da busassun kifaye manya da kanana guda dubu daya da dari biyar da biyar, buhunan shinkafa na gida guda goma sha bakwai da buhunan wake biyu.
Nuradeen ya bayyana cewa wannan kamen yana nuna jajircewa da kokarin da Hukumar ta ke yi na aiwatar da manufar rufe iyakokin kasar nan da nufin kare tattalin arzikin kasa da kuma tabbatar da samar da abinci.
“Tsarin fasahohin na lalata halaltattun hanyoyin kasuwanci yana haifar da hadari ga lafiyar jama’a da kuma hana gwamnati samun kudaden shiga kamar yadda ake bukata.”
Hukumar kwastam ta nanata kudurin ta na yakar ayyukan fasakwauri a duk kafafin shigowa kasar nan.
Nuradeen ya bukaci jama’a da su samar da sahihin bayanai domin dakile safarar kayayyakin ba bisa tsarin doka ba.
Ya kara jaddada kudurin hukumar na dakile ayyukan haramun domin kare masana’antu na cikin gida da kuma inganta samar da abinci.
A halin da ake ciki, Mataimakin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, ta shiyyar B, IQ Ibudu, ya yi kira ga al’ummar yankin Maigatari da su yi taka-tsan-tsan tare da mutunta dokar rufe iyakokin kasa kamar yadda ƙungiyar tattalin arziƙin yammancin Afirka ECOWAS ta bayar.
Hukumar ta ce gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin magance kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da ke addabar kasar.
Har ila yau, Kwanturola na shiyar Kano da Jigawa, Dauda Ibrahim Chana, ya bukaci al’ummomin kan iyaka da su baiwa hukumar da sauran jami’an tsaro hadin kai domin kare kan iyakokin su.
Ya kuma ba su tabbacin cewa Ma’aikatar ta dukufa wajen ganin ta magance bukatun su, musamman ta fuskar huldar jama’a.