Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta fara mayar da kayan abinci daban-daban da ta kama daga hannun ‘yan kasuwa a yankunan kan iyaka a jihar Katsina.
Hakan dai ya yi dai-dai da umarnin da Shugaban Ƙasa ya bayar na cewa hukumar ta mayar da duk kayan abincin da aka kama a yankunan kan iyakokin ƙasar da sharaɗin sayar da su a ƙasar.
Kwanturolan Rundunar ‘Yan Sandan jihar Katsina, Mohammed Umar, ya ce an mayar da sama da tireloli shida na hatsi iri-iri da aka kama a kan hanyar Kwangwalam-Mai’adua ga masu su.
“Kwanturola Janar na Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, a ziyarar aiki da ya kai Katsina, ya miƙa umarnin Shugaban Ƙasa na mayar da kayan abincin da aka tsare ga masu su da sharaɗin za a sayar da su a kasuwannin Nijeriya,” inji shi.
Sai dai Shugaban Ma’aikatan Gwamna Radda, Hon. Jabiru Tsauri, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin da Gwamnan ya kafa domin magance tashin farashin kayayyakin abinci da kuma magance matsalar riƙon kayayyaki, ya ce kayayyakin abincin da aka sako za a sayar wa mazauna jihar Katsina ne kawai.