Back

Hukumar Kwastam ta musanta zargin sanadin mutuwar wani matashi a Katsina

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta musanta cewa tana da hannu a mutuwar wani matashi a garin Jibiya cikin jihar Katsina a ranar Asabar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Maiwada ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a yayin da yake mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin.

A cewar mazauna garin na Jibiya, wani direban motar kasuwanci ne ya kashe yaron a ranar Asabar din nan da ta gabata a garin, wanda wasu Jama’a suka dauka cewa jami’an kwastam ne suka bi shi, suka yi sanadiyyar raba shi da ran na sa.

wani mazaunin garin, wanda aka sakaya sunan sa, yace direban motar da yayi sanadin kisan matashin,  ya ambaci jami’an kwastam din ne domin ya tsira.

Mazauna yankin sun ci gaba da cewa, direban motar, Mai kirar J5 Peugeot ya afkawa wasu da ke wucewa a kusa da makarantar firamare ta Tundun Wada, Jibia ne inda yayi sanadin rasuwar yaron.

Duk da hakan, da yawa daga cikin mazauna yankin da suka yi magana kan sharadin a sakaya sunayen su, sun yi ikirarin cewa hatsarin ya faru ne sakamakon kasancewar jami’an kwastam a yankin.

Da yake Karin bayani game da aukuwar tsautsayin, Maiwada ya ce ya zama dole hukumar ta kwastam ta wayar da kan al’umma bisa wannan zargin da bata san hawa ba balle sauka. 

A bayanin sa “An ja hankalin mu kan mummunar asarar Rai da aka yi a yankin iyakar Jibia da ke Jihar Katsina a ranar Asabar 3 ga Fabrairu, 2024. Muna mika ta’aziyyar mu ga iyalai da ‘yan uwa na matashin da aka yi rashi.”

Kakakin hukumar kwastam din ya ce babu wani jami’in su da ya tuka motar da take da gyara wadda har zata kubuce tayi hadari a wannan ranar.

“Yana da kyau a yi maganin rashin bayyana gaskiya da ke yawo a kafafen yada labarai dangane da rahoton kashe matashin da wani direban mota J5 ya yi.”

A cewar sa, “Muna so mu fayyace cewa jami’an mu, ba su tuka motar J5 ba ko kuma sun tare ta, ko irin ta a lokacin da lamarin ya faru ba, sabanin yadda wasu ‘yan jarida ke zargin jami’an mu da hannu cikin lamarin. Rahotannin farko sun nuna cewar motar da yayi hadarin, jigilar wake take yi a lokacin, kuma a halin yanzu direban yana hannun ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.”

A cikin sanarwar da babban kwanturolan hukumar ta Kwastam ya fitar, Adewale Adeniyi, ya nanata kudurin sa na ingan ta huldar da ke tsakanin al’umma tare da gudanar da ayyukan yaki da fasa kwauri ba tare da an samu asarar rai ba.

Adeniyi ya kuma bukaci jama’a da su bi umarnin gwamnati tare da bawa jami’an tsaro hadin kai domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.

“muna rokon dukkan masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankalin su. Muna kuma matukar godiya da ci gaba da hadin gwiwar da al’ummomin kan iyakoki ke bayarwa yayin da muke aiki tare don magance kalubale da inganta tsaro da yalwa ga kowa da kowa,” In ji Adeniyi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?