Back

Hukumar Kwastam ta soke hukuncin kashi 25 kan motocin da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba

Muƙaddashin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Mista Adewale Adeniyi

Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) ta ƙaddamar da dama na kwanaki 90, daga ranar 4 ga Maris 2024 zuwa 5 ga Yuli, 2024, domin daidaita harajin shigo da kayayyaki kan takamaiman nau’ikan motoci.

Abdullahi Maiwada, kakakin hukumar NCS, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya cewa, umarnin ya fito ne daga Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Harkokin Tattalin Arziƙi, Wale Edun.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa: “Don sauƙaƙa wahalhalun tattalin arziƙi da ƙarfafa bin doka, Mai Girma Minista kuma Ministan Kula da Harkokin Tattalin Arziƙi ya amince da dakatar da hukuncin kashi 25% da aka sanya a baya, baya ga harajin shigo da motocin da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba.

“An ƙarfafa masu ruwa da tsaki, ciki har da masu abin hawa, masu shigo da kaya, da wakilai, da su yi amfani da wannan damar don daidaita biyan harajin shigo da kaya a cikin wa’adin kwanaki 90.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?