Back

Hukumar Sufurin Jiragen Sama Ta Sake Buɗe Titin Filin Jirgi na Legas Bayan Watanni Sha Ɗaya Da Rufewa

Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya, FAAN, ta sake buɗe titin jirgin sama mai lamba 18R/36L a filin jirgin Murtala Muhammed International Airport (MMIA), da ke Legas watanni sha ɗaya bayan rufewar don gyarawa.

An kuma Bude Hanyoyin titin jiragen sama na ƙasa da ƙasa, ta yadda za a rage nauyi a kan titin 18L/36R na cikin gida a ranar Asabar.

Jirgin Kenya Airways ne ya fara sauka a kan titin jirgin a ranar Asabar kuma an yi masa maraba da ban ruwa.

Hukumar ta FAAN a watan ukun shekarar da ta gabata, ta sanar da rufe titin jiragen sama na ƙasa da ƙasa 18R da 36L a filin jirgin Murtala Muhammed da ke Legas domin gyara su.

FAAN ta ce za a rufe titin jiragen har na tsawon makonni takwas domin gyara su.

Kamar yadda yake kundhe a sanarwar: “Wannan domin sanar da jama’a ne cewa an rufe titin jirgin sama mai lamba 18R/36L na filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas na tsawon makonni takwas domin gudanar da gyare-gyare.”

Rufe titin jirgin ya shafi zirga-zirgar jiragen sama da jadawalin kamfanin jirgin saman, da kuma ƙara farashin kamfanonin jiragen sama yayin da suka ƙona mai da yawa da kuma haifar da tsaikon fasinjoji.

Titin jirgin da aka sake buɗewa na 18R/36L yana da tsayin 3,900 m (ƙafa 12,794) da faɗin 60 m ( ƙafa 197).

Manajan daraktan hukumar ta FAAN, Olubunmi Kuku, yayin wani rangaɗin da ta kai kwanan nan na zirga-zirgar ababen hawa a MMIA, ta yi nuni da cewa sake buɗe titin jirgin sama na 18R, na iya faruwa da wuri fiye da yadda ake tsammani.

Kuku ta bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin gaggauta sake buɗe titin ta hanyar wucin gadi da Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya, NAMA, ta haɗa.

A shirye-shiryen sake buɗe titin jirgin, MD na FAAN ta yi ƙarin haske game da haɗa gwiwa da Masu Kamfanin Jiragen Sama na Najeriya (AON) da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) don tabbatar da cewa an dawo da ayyukansu cikin sauƙi da kuma kan lokaci.

Kuku ta bayyana ƙwarin guiwar sake buɗewan, inda ta bayyana cewa masu ruwa da tsaki za su iya hasashen faruwar lamarin nan ba da daɗewa ba, tare da samun cikakken goyon bayan minista da sakatare na dindindin.

“Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da ɗan kwangilar, kuma tare da goyon bayan minista da sakatare na dindindin, muna sa ran sake buɗewa cikin ‘yan makonni masu zuwa. Masu ruwa da tsakin mu sun yi haƙuri, kuma mun himmatu wajen rage jinkirin. Yayin da shirin farko ya kasance na rufewa makonni shida, an samu jinkirin da ba a zata ba, amma muna yin iya ƙoƙarinmu don hanzarta aiwatar da aikin.” Inji ta.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?